1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta fara aika dakarun ta a Jamhuriya Demokradiyar Kongo

July 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bur0

A yau ne Jamus ta fara aika dakarun ta, a Jamhuriya Demokradiyar Kongo, a shirye shiryen zaɓen da za a gudanar ranar 30 ga watan da mu ke ciki.

Sojojin Bundeswehr guda 60 daidai, su ka tashi yau, daga filin saukar jiragen samar sojoji, na birnin Klon, zuwa Librebville,a ƙasar Gabon, inji kakakin wannan runduna.

Sojojin za su haɗuwa da sauran takwarorin su na ƙungiyar EU.

Kamar yadda shawara ministocin harakokin tsaron ƙungiyar EU ta tsaida, wani sashe na sojojin zai kasance a Librevile, cikin shirin ko ta kwan, a yayin da za a jibge wani gumen, a birbni Kinshasa.

A farkon watan da mu ke ciki, ministan tsaron Jamus Franz Josef Yung, ya kai ziyara a jamhuriya Demokradiyar Kongo, da kuma Gabon, inda ya tantana da hukumomin ƙasashen 2,a game da rundunar ƙungiyar gamaya turai.

A jimilce Jamus zata aika dakaru 780 a cikin wannan runduna