1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta haramta taba sigari a maáikatun gwamnati

December 14, 2006
https://p.dw.com/p/BuY1

Majalisar gudanarwar gwamnatin tarayyar Jamus ta haramta shan taba sigari a dukkanin ofisoshin gwamnati da kuma motocin haya. Matakin ya biyo bayan sakamakon tattaunawa tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya a game da dokokin da suka shafi taba sigari. Bayan ganawa da shugabar gwamnati Angela Merkel gwamnonin jihohi goma sha shida na tarayyar Jamus sun sanar da aniyar tsara dokoki na bai ɗaya a game da taba sigari a watan Maris na sabuwar shekara.