1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta koka game da yawan fashin jiragen ruwa a gabashin Afirka

April 11, 2010

Ministan harkokin wajen Jamus ya buƙaci kawo ƙarshen fashin jiragen ruwa a ƙasar Somaliya

https://p.dw.com/p/MtE8
Westerwelle a DjiboutiHoto: dpa

Ministan kula da harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, wanda ke kammala rangadin yini biyar a Nahiyar Afirka, ya buƙaci a shawo kan barazanar fashin jiragen ruwar da ake fuskanta a yankin gabashin Afirka. Westerwelle ya yi wannan furucin ne a lokacin ganawar sa da shugaban ƙasar Djibouti Isma'il Umar Guelleh, da kuma ministan kula da harkokin wajen ƙasar Mahmud Ali Yusuf, inda suka taɓo matsalar data dabaibaye Somaliya, wadda ke makwabtaka da Djibouti. Westerwelle ya ce, matsalar manuniya ce ga buƙatar ƙasashen Duniya su haɗa kai wuri guda wajen tallafawa Somaliya, inda jama'ar ƙasar da dama suka mayar da fashin jiragen ruwa da kuma yin garkuwa da jama'a a matsayin hanyar samun kuɗin shiga.

A baya bayannan ne hukumomin Jamus dake Berlin - babban birnin ƙasar, suka nuna ƙudurin buɗe ofishin jakanci a Djibouti, wadda 'yan ƙaramar ƙasa ce dake Nahiyar Afirka. Kafin zuwa ƙasar Djibouti dai Westerwelle ya ziyarci ƙasashen Tanzania da kuma Afirka Ta Kudu a ziyarar yini biyar ɗin da ministocin gwamnatin Jamus biyu, wato na harkokin ƙetaren da kuma ministan kula da harkokin raya ƙasa a Jamus, Dirk Niebel

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Muhammad Abubakar