1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta nuna adawa da huldar EU a Turkiya

Gazali Abdou Tasawa
August 29, 2017

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi watsi da yunkurin EU na shigar daTurkiya a cikin tsarin aikin kwastam ko na kasuwancin na bay daya na kasashen Turai sabili da yadda Turkiya ba ta kiyaye hakkin dan Adam.

https://p.dw.com/p/2j22w
Deutschland Wahlkampf CDU Sachsen-Anhalt mit Bundeskanzlerin Angela Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Pförtner

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi watsi da aniyar shigar daTurkiya a cikin tsarin aikin kwastam ko na kasuwancin na bay daya na kasashen Turai matsawar ba ta ta nuna wani ci gaba ba a fannin kiyaye hakkin dan Adam ba.

"Merkel ta ce a halin yanzu ci gaban Turkiya na tafiya a baibai ne, ba za mu ce mun yanke kauna ba da ita. amma a yanzu dangane da batun hulda  da ita a fannin tattalin arziki ba ni ga za mu iya ba da izinin a soma tattaunawa da ita matsawar babu sauyi daga halin da ake ciki a kasar a yanzu"

Tun a shekara ta 2005 ne dai kungiyar EU ta soma tattaunawa da Turkiya kan batun shigarta a cikin kungiyar , sai dai lamarin ke tafiyar hawainiya a bisa zargin da kasashen Turan ke yi wa Turkiyar na kin mutunta hakkin dan Adam.