1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta sake bude ofishin jakadancinta a birnin Monrovia

October 25, 2005
https://p.dw.com/p/BvNu
Bayan wa´adi na shekara 8 Jamus ta sake bude ofishin jakadancin ta a kasar Liberia dake Yammacin Afirka. Wannan matakin dai ya sa yanzu tarayyar Jamus ta zama ta farko a jerin kasashen KTT da ta sake bude ofishin jakadanci a birnin Monrovia. Wata sanarwa da ma´aikatar harkoin wajen Jamus a birnin Berlin ta bayar ta ce sake bude ofishin jakadancin dai na matsayin wata gudummawa da kasar ta Jamus zata bayar a kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Liberia. A lokacin yakin basasan Liberia a cikin watan yunin shekarar 1997 Jamus ta rufe ofishin jakadancin ta a Monrovia.