1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta shiga Kwamitin Sulhu

Tijani LawalOctober 13, 2010

Jamus ta yi nasarar samun kujerar karɓa-karɓa na wa´adin shekaru biyu a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/Pdca
Zauren taron kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin DuniyaHoto: cc-by-sa-Patrick Gruban

Wannan ya biyo bayan wata ƙuri'ar da mambobin ƙasashe192 da ke babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya su ka kaɗa a New York. A zagaye na farko na zaɓen Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya, Jamus ce kaɗai ta ƙetare daga zaɓen rukunin da ake kira yammacin Turai da kewaye bayan da ta sami ƙuri'u 127 a cikin 128 da kowace ƙasa ke buƙata kafin ta samu kujerar wakilci a kwamitin. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta faɗa wa manema labarai cewa gwamnatin na matuƙar farin cikin sakamakon, kuma ƙasar za ta yi aiki tuƙuru, wajen ganin an aiwatar da gyare-gyaren da kwamitin ke yi. Merkel ta ƙara da cewa:

Angela Merkel in Rumänien
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa

"Wannan wata karramawa ce a ɓangarenmmu, ta samun amincewa daga ƙasashe masu yawa. Sai dai kuma kamar yadda yake akan kowa ne batu, muna da alhakin sauke nauyin daya rataya a wuyammu, na taka rawa a dangane da tabbatar da tsaro da samar da mafita a yankuna da ake fama da rigingimu."

Jamus tana ɗaya daga cikin ƙasashen da ke kan gaba wajen bai wa Majalisar Ɗinkin Duniya gudunmawa, tare da Indiya, Japan da Brazil, waɗanda kuma ake gani su suka cancanta a bai wa dauwamammiyar kujera a kwamitin sulhun, idan har ƙasashe mambobi suka amince da a ƙara yawan kujerun da kwamitin ke da su, saboda an shafe fiye da shekaru goma ana tattaunawa domin ƙara yawan ƙasashe mambobi amma har yanzu ba a ci nasarar hakan ba.

A yayin da yake bayyana farincikin sa da wannan lamari, ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ce duk ayyukan ƙasar za su kasance a bayyane, kuma kunnuwan su zasu kasance a buɗe domin tattaunawa da duk mai neman shawara. Westerwelle ya ce:

Bundesaußenminister Westerwelle bei der UN
Ministan harkokin wajen Jamus Guido WesterwelleHoto: picture alliance/dpa

"Muna farin cikin ganin cewa ƙudurorin mu na samar da zaman lafiya, tsaro, kare muhalli, kwance ɗammara, rage yaɗuwar makaman nukiliya da ma manufofin harkokin waje, za mu cigaba da ƙarfafa su yanzu a Kwamitin Sulhu."

Ƙasar India ta ce za ta ba da fifiƙo wajen aiwatar da manufofin kwamtin sulhun a yayin da ita ma Afirka ta Kudu ta ce ɗaya daga cikin abubuwan da za ta ba karfi shi ne ɗage ƙarar shugaban Sudan Omar-Albashir, da ke gaban kotun ƙasa da ƙasa ta hukunta miyagun laifuka, wanda ke tuhumarsa da aikata kisan ƙare dangi a yankin Dafur da ke ƙasar Sudan. Guido Westerwelle ya yi ƙarin haske dangane da rawar da Jamus za ta taka a wannan karon:

"Matsayin Jamus a nan shine ta taimaka wajen samar da daidaituwa tsakanin daulolin duniya. A ra'ayi na, yankunan Latin Amurka, Afirka, da Asiya ba su da wakilcin da ya dace da su a Kwamitin Sulhu, saboda haka, Jamus tana so ta ga an canza wannan."

Ƙasashe biyar da za su yi wa'adin shekaru biyu a wannan karon sun haɗa da Bosnia, Brazil, Gabon, Lebanon da Najeriya. Ƙasashen da zasu sauka kuma a ƙarshen wannan shekarar sun haɗa da Austria, Turkiyya, Mexico, Japan da Uganda.

Mwallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Ahmad Tijani Lawal