1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta yi kira ga manyan kasashen duniya da su rage karfinsu na nukiliya

June 17, 2006
https://p.dw.com/p/ButZ
Jamus ta yi kira ga manyan kasashen duniya masu karfin makaman nukiliya da su rage karfinsu na nukiliya a daidai lokacin da suke kira ga Iran da ta yi watsi da shirin ta na nukiliya. A cikin wata hira da mujallar Der Spiegel, ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce kamata yayi kasashe 5 masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD wato Amirka, Rasha, China, Birtaniya da kuma Faransa da su kara nuna sassauci a takaddamar da ake yi game da shirin nukiliyar Iran. Jamus wadda ba ta mallakar makamin nukiliya hade da sauran kasashe biyar membobin dindindin a kwamitin sulhu sun gabatarwa gwamnatin Teheran wani tayin taimako idan Iran ta daina sarrafa sinadarin uranium.