1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta zargi Turkiya da leken asirin Gülen

Gazali Abdou Tasawa
March 28, 2017

Ministan cikin gida na jihar Lower Saxony a Jamus Boris Pirtorius, ya bayyana cewa yanzu haka mahukuntan Ankara sun bukaci Berlin ta taimaka masu ga leko asirin mutane da kungiyoyi 300 magoya bayan Gülen a Jamus.

https://p.dw.com/p/2a8dn
Niedersachsens Innenminister Boris Pistorius zu Abschiebungen
Hoto: picture alliance/dpa/P. Steffen

Jamus ta zargi mahukuntan Turkiya da aiwatar da leken asiri kan magoya bayan Fetullah Gülen shahararren malamin nan dan adawa dake zama gudun hijira a kasar Amirka. Ministan cikin gida na jihar Lower Saxony a nan Jamus, Boris Pirtorius wanda ya gabatar da wannan zargi, ya bayyana cewa yanzu haka mahukuntan Ankara sun bukaci takwarorinsu na Berlin da su taimaka masu ga leko asirin mutane da kungiyoyi 300 na 'yan Turkiyar mazauna kasar ta Jamus wadanda suke zargi da kusanci da kungiyar Fetullah Gülen, mutuman da Ankarar ke zargi da kitsa juyin mulkin watan Yulin shekarar bara da ya ci tura a kasar ta Turkiya. 

Ministan cikin gida na jihar ta Lower Saxony ya yi kira ga gwamnatin Angela Merkel wacce a baya bayan nan ta yi sa in sa da Turkiya kan batun shirya zaben raba gardama na ranar 16 ga watan Aprilu, da ta dauki matakin da ya dace kan mahukuntan kasar ta Turkiya.