1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus tace a shirye take ta karawa ran takunkumi

September 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuB0

Kasar Jamus tace a shirye take ta kara lakaba takunkumi akan kasar Iran kann shirinta na nukiliya.Mataimakin ministan harkokin waje Gernot Erler yace muddin dai Iran ta ki amincewa da bukatun kasashen duniya na dakatar da inganta sinadarin uraniyum dole ne zaa ci gaba da matsa mata lamba.

Erler yace a Jamus da kasashe kawayenta a shirye suke su tattauna tare da nufin yanke shawara a kann wannan batu.

A ranar Jumaa Jamus zata gana da manyan kasashe 5 masu ikon darewa kujerar naki a komitin sulhu inda zasu tattauna sabon kudirin komitin sulhu akan kasar Iran.Idan sun amince kann wannan takunkumi,shine zai zama kudurin takunkumi na uku kan Iran bayan biyu da aka lakaba mata a watannin desamba da maris.