1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta ƙara ba da taimakon kuɗi don tallafa wa Somaliya

YAHAYA AHMEDMarch 17, 2006

Jamus ta yi wa Ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta Red Cross alkawarin ba ta ƙarin taimakon kuɗi don ci gaba da aikin ba da taimakon agaji da take yi a ƙasar Somaliya. Ministan ma'ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya ƙasashe ta tarayya, Heidemarie Wiecorek-Zeul ce ta bayyana haka a birnin Berlin, bayan ganawar da ta yi da shugaban ƙungiyar.

https://p.dw.com/p/BvTi
Heidemarie Wieczorek-Zeul
Heidemarie Wieczorek-ZeulHoto: dpa

A duk inda sauran ƙungiyoyin sa kai na ba da taimakon agaji suka kai haddin ƙoƙarinsu, ba su san kuma inda za su mai da alƙibla ba, nan ne ake ganin muhimmancin Ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta Red Cross a zahiri. Ko a gidajen yari da sansanonin da kowa ba ya samun damar leƙawa cikinsu ne, ko kuma a yankunan da yaƙi ya yi tsanani ne, ita dai ƙungiyar ta Red Cross na iya ɗaukar kasadar kutsawa don ta kai wa waɗanda suka galabaita taimakon agaji. Duk da irin wannan namijin ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi dai, ita ma ta dogara ne kacokan kan taimakon kuɗaɗen da take samu daga gamayyar ƙasa da ƙasa.

Sabili da haka ne kuwa, shugaban ƙungiyar, Jacob Kellenberger, wanda asalinsa ɗan ƙasar Switzerland ne, ya bayyana matuƙar gamsuwarsa da alkawarin da ya samu daga ministan ma’ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya ƙasashe ta tarayyar Jamus, Heidemarie Wiezoreck-Zeul, a ganawar da suka yi jiya a birnin Berlin.

Jamus dai, bisa cewar ministan ba da taimakon raya ƙasashenta, Heidemarie Wiecoreck-Zeul, a shirye take ta ba da ƙarin taimako na Euro dubu ɗari 2 da 50 ga ƙungiyar ta Red Cross, a yunƙurin da take yi na agaza wa al’umman yankunan da ke fama da yunwa a ƙasar ta Somaliya. Tuni dai, Hukumar Ciyad da Duniya da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta bai wa ƙungiyar ta Red Cross taimakon kuɗi na kimanin Euro dubu ɗari 7 da 50, a ƙarƙashin wannan shirin dai na agaza wa Somaliyan. Ban da dai yankin Darfur na ƙasar Sudan, halin da ake ciki a ƙasar Somaliya, ya fi na ko’ina muni a nahiyar Afirka, inji shugaban kwammitin ƙasa da ƙasa na ƙungiyar ta Red Cross. Ya ƙara da cewa:-

„A can, wato Somaliyan, muna fama ne da yaƙe-yaken basasa da kuma wani mummunan fari. Bugu da ƙari kuma, ƙungiyoyin sa kai ƙalilan ne ke aiki a yankunan da matsalar ta fi tsanani. Zan iya cewa, kusan mu kaɗai ne ma ke da wakilci a can.“

Ban da dai batun Somaliya, Jacob Kellenberger, ya kuma tattauna halin da fursunoni ke ciki da matsalolin da ake huskkanta a gidajen yari a sassa daban-daban na duniya. A cikin shekarar bara kawai, jami’an ƙungiyar sun kai ziyara fiye da dubu 2 a gidajen yari a ƙasashe 80 na duniya, inda ake tsare da kusan fursunoni dubu 60, inji Kellenberger:-

„Muna kai waɗannan ziyarce-ziyarcen ne, don mu gano wa idanunmu yadda halin gidajen yarin ke ciki da kuma yadda ake kulawa da fursunonin. Idan muka ga cewa, an saɓa wa ƙa’idojin ƙasa da ƙasa, to sai mu yi katsalandan, ko da ma a kafar ƙoli ce ta ƙasar da lamarin ya shafa. Sai dai, a galibi, ba ma bayyana ƙararrakinmu a bainar jama’a. Amma a gaban hukumomin da batun ya shafa, muna bayyana duk irin abin da muka ga bai da ce a yi ba, mu kuma dage kan cewa, sai an yi gyara.“

A nan dai, ba gaban hukumomin ƙasashen da ba sa bin mulkin dimukraɗiyya kaɗai shugaban na Red Cross ke nufi suke kai ƙararrakin take hakkin fursunoni ba. Har da ma a ƙasashe kamarsu Amirka, inji shi, wadda ta kafa sansanoni don tsare fursunonin da dakarunta suka kame wai a fafutukar yaƙan ta’addanci.