1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta ci tarar kamfanonin sada zumunta

Gazali Abdou Tasawa
April 5, 2017

Jamus ta dauki wata sabuwar doka ta cin tarar kudi daga Euro dubu biyar zuwa dubu 50 ga kamfanonin sada zumunta na zamani, da za a kama da laifin kin daukar matakin yaki da wallafa labaran karya da nuna kyama.

https://p.dw.com/p/2ajZ1
Screenshot der Facebookseite der Stadt Berlin
Hoto: Facebook

Kasar Jamus ta kaddamar da wata sabuwar doka wacce ta tanadi hukuncin tarar kudi daga Euro dubu biyar zuwa dubu 50 ga kamfanonin sada zumunta na zamani, da za a kama da laifin kin daukar matakin yaki da wallafa labaran karya da nuna kyamar jama'a musamman irin wadanda masu akidar Nazi ke yadawa a kasar a saman shafukan sada zumuntar. 

Taron majalisar ministocin kasar ta Jamus ne ya amince da wannan doka wacce ta jima tana haifar da muhawara a bisa fargabar da jama'a ke yi ta iya kasancewa ta tauye fadin albarkacin baki a kasar. 

A cikin wata sanarwa da fadar shugabar gwamnatin kasar ta Jamus Angela Merkel ta wallafa kan wannan doka, ta bayyana cewa idan har ba a dauki matakin yaki da masu yada akidar kyama ko labaran karya tare da gurfanar da su a gaban kuliya ba, to kuwa sukan iya kasancewa babbar barazana ga zaman lanfiyar al'ummar kasar ta Jamus. Amma dokar za ta soma aiki ne bayan  majalisar dokokin kasar ta Jamus ta sanya mata hannnu a nan gaba.