1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta dauki karin 'yan gudun hijira

Yusuf BalaAugust 23, 2016

Kididdiga ta baya-bayan nan dai ta nunar da cewa kusan 'yan Iritiriya 4000 ne da 'yan Siriya sama da 700 da 'yan Iraki sama da 600 suka isa Italiya a watanni bakwai na farkon wannan shekara.

https://p.dw.com/p/1Jnba
Türkei syrische Flüchtlinge laden Merkel ein
Danganawa zuwa Jamus dai na zama cikar buri ga dubban 'yan gudun hijiraHoto: picture-alliance/AA/K. Kocalar

Jamus ta amince ta kara yawan daruruwan 'yan gudun hijira da za ta dauka bayan da suke jibge a zaman jiran tsammani a Italiya. Wani abu da ke kara nuna alamu na sake farfado da shirin Kungiyar Tarayyar Turai na rarraba bakin a tsakanin kasashensu a cewar Angelino Alfano da ke zama ministan harkokin cikin gida na Italiya a ranar Talatan nan.

A kokarinta na ganin an rage radadi da kasashen da suka fi karbar 'yan gudun hijira, hukumar Kungiyar Tarayyar Turai a shekarar bara ta fito da wani tsari na janye dubban 'yan gudun hijira da ke jibge a Italiya da Girka dan rabasu a tsakanin kasashen na Turai.

Karkashin wannan shiri dai kusan 'yan gudun hijira 40,000 ne daga Italiya za a raba su zuwa wasu kasashe cikin shekaru biyu, sai dai kawowa yanzu wasu daruruwa ne kawai suka samu dama ta tsallakawa wasu kasashe na Turai saboda halin ko in kula da wasu kasashen na Turai kan nuna kan batun na bada mafakar siyasa ko daukar 'yan gudun hijira.