1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta tura karin sojoji 550 kasashen Mali da Iraki

Kamaluddeen SaniJanuary 6, 2016

Wannan matakin da gwamnatin Jamus ta dauka na daga cikin gudumawar da kasar ke bayarwa a yakin da ake da kungiyoyin 'yan tarzoma.

https://p.dw.com/p/1HZQY
Symbolbild Bundeswehr in Mali
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Majalisar zartarwar gwamnatin Jamus ta yanke shawarar aikewa da sojojin kasar su 550 domin ayyukan yakar kungiyoyin mayaka masu tsattsauran ra'ayi a kasashen Mali da kuma Iraki.

Sojojin na tarayyar Jamus za a tura su zuwa Mali domin tallafa wa dakarun Faransa gami da bayar da horo na musamman ga Kurdawa da ke bata kashi da mayakan IS a Iraki.

Ministar harkokin tsaron Jamus Ursula von der Leyen ta yi nuni da cewar dole ne su yi aiki kafada da kafada da Faransa domin tallafa musu.

Yanzu haka dai majalisar ta amince da tura sojojin sama da 500 wadanda ke jiran amincewar majalisar dokokin tarayyar ta Jamus nan da 'yan makonni da ke tafe.