1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta kauce wa kaka-gida a Kungiyar EU

Yusuf Bala Nayaya MNA
February 10, 2018

Jamus bai kamata ta kasance sai abin da take so za a yi ba kan harkokin tattalin arzikin kasashe kawayenta a Kungiyar Tarayyar Turai a cewar dan jam'iyyar Social Democrats Olaf Scholz.

https://p.dw.com/p/2sRvB
Deutschland Olaf Scholz, SPD
Olaf Scholz da ake fatan ya zama ministan kudi a JamusHoto: picture-alliance/dpa/C. Charisius

Olaf Scholz, da ake fatan ya zama ministan kudi a Jamus nan gaba a sabuwar gwamnatin hadaka ya bayyana haka ne a tattaunawar da ya yi da mujallar Der Spiegel da aka wallafa a wannan rana ta Asabar, lamarin da ke nuna alamun cewa Jamus za ta dan sassauto kan tsauri da take da shi idan ana magana ta harkokin kudi na kasashen da ke karkashin kungiyar ta EU.

Scholz ya ce ba za su kasance 'yan kama karya ba ga sauran takwarorinsu na EU ta yadda sai yadda suke so za a yi ta fiskar tattalin arzikin kawayensu. Magajin gari daga birnin Hamburg, Scholz shi ake fatan zai maye gurbin Wolfgang Schaeuble wanda shekaru takwas da ya yi a ministan kudi a Jamus an ga tsauri wajen tsuke bakin aljihu.