1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta kori baƙi masu laifi

Abdourahamane HassaneJanuary 27, 2016

Gwamnatin ƙasar Jamus ta amince da wani shirin doka wanda zai kai ga korar baƙin da aka samu da laifin cin zarafi wasu matan a lokacin bukukuwan shiga sabuwar shekara da aka yi a cikin watan jiya.

https://p.dw.com/p/1Hki6
inistan shari'a na Jamus Heiko Maas
Ministan shari'a na Jamus Heiko MaasHoto: picture-alliance/dpa/J. Carstensen

Ƙudirin wanda ministan shari'a Heiko Maas da kuma ministan cikin gida Thomas de Maiziere suka gabatar.Nan gaba ne za a miƙashi ga majalisar dokokin ƙasar watau Bundastag domin ta yi mahawara ta kuma yanke shawara a kansa

mata kamar dari shida suka gabatar da ƙara na cin zarafinsu a birnin Cologne da kuma wasu garuruwan a lokacin bukukuwan. A binciken da 'yan sanda suka gudanar yawancin waɗanda suka aikata laifukan 'yan ci rani na yanki arewacin Afirka.