1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta tasa keyar bakin haure

February 22, 2017

Jamus za ta mayar da masu neman mafaka wadanda ba a amince da takardunsu ba zuwa kasashensu na asali karkashin wani shirin da gwamnatin ta amince da shi.

https://p.dw.com/p/2Y6NH
Deutschland PK Thomas De Maziere über Anschlag in Berlin
Ministan cikin gida na Jamus Thoma de MaiziereHoto: Getty Images/AFP/J. McDougall

Majalisar gudanarwar Jamus ta amince da wani shiri da zai saukaka mayar da yan gudun hijirar da ba'a amince da takardunsu ba zuwa kasashensu na asali


A karkashin wani kudirin doka da aka zartar a wannan larabar, matakin zai bada damar mayar mutane da yawa wadanda ba'a amince da takardunsu na neman mafaka a kasar ta Jamjus ba kamar yadda ministan cikin gida Thomas de Maiziere ya baiyana.

" Yace muna tsammanin karin hukunci mara dadi, abin da ke nufin cewa yan gudun hijira da dama za su bar kasar a wannan shekarar. A saboda haka yana da muhimmanci mu tabbatar da cewa wadannan mutane da ba'a amince da takardunsu ba sun bar kasar mu don radin kansu za kuma mu bada muhimmanci wajen tallafa musu"

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ke tunkarar zabe a watan Satumba ta sha nanata bukatar daukar matakan da suka dace na ganin wadanda basu da izinin zama sun bar kasar.