1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus zata aike da dakarun sojin kiyaye zaman lafiya izuwa Kongo

June 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buvr

A yau alhamis ne ake sa ran majalisar dokokin Jamus ta Bundestag zata tattabar ta amannarta ta yarda da tura dakarun sojin kiyaye zaman lafiyar kasar izuwa kasar Congo.

Mahukuntan na Jamus dai na kokarin aikewa da dakarun soji a kalla 780 ne izuwa kasar ta Kongo, karkashin laimar kungiyyar Eu, a bisa bukatar yin hakan daga Mdd.

Rahotanni dai sun nunar da cewa dakarun sojin na Jamus zasu taimakawa kasar ta Kongo ne wajen tattabatar da doka da kuma oda a lokacin zaben gama gari, da kasar ke shirin yi nan bada dadewa ba.

Wannan zabe dai na ´a matsayin irin sa na farko ne a tsawon shekaru 40 da suka gabata, a wannan kasa data sha fama da yakin basasa.

Koda a jiya ma dai , bayanai sun shaidar da rasuwar mutane 80, bayan wani dauki ba dadi da akayi a tsakanin dakarun sojin kasar da kuma tsagerun yan tawaye a yankin Ituri.