1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus zata ba da gudunmawar sojoji ga rundunar EU a Kongo

January 29, 2006
https://p.dw.com/p/BvAO

Ministan tsaron tarayyar Jamus Franz Josef Jung ya ce dakarun rundunar sojin kasar wato Bundeswehr ba zasu taka wata muhimmiyar rawa a cikin rundunar da KTT ke shirin turawa JDK don marawa sojojin MDD a aikin wanzar da zaman lafiya ba. Herr Jung ya fadawa jaridar FAZ ta ranar lahadi cewa Jamus zata yi bakin kokarinta don taimakawa rundunar ta kungiyar EU. Kungiyar dai na shirin girke sdakarun kimanin dubu daya da 500 ciki har da sojojin Jamus a Kongo. Kalaman na ministan tsaron sun zo ne a daidai lokacin da wata tawagar kungiyar EU ke shirin zuwa Kongo don duba halin da ake ciki kafin girke dakarun wadanda zasu marawa sojojin MDD kimanin dubu 16 da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Kongo.