1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus zata shugabanci G8 daga farkon janairu mai zuwa

October 18, 2006

A karkashin shugabancinta ga G8 Jamus zata mayar da hankali wajen daidaita gibin ciniki na kasa da kasa da raya makomar Afurka

https://p.dw.com/p/Btxh

Ta la’akari da matsayin da taron kolin kasashen na G8 ke da shi a duniya Jamus ke da niyyar bai taron taken: Bunkasar tattalin arziki da sanin ya kamata, kamar yadda aka ji daga Ulrich Wilhelm mai magana da yawun gwamnati, wanda yace hakan na ma’anar wasu batutuwa ne guda biyu:

“Bai wa dangantakar tattalin arziki ta kasa da kasa wani sabon fasalin da ya dace da kuma raya makomar nahiyar Afurka.”

Da farko dai gwamnati na tattare da damuwa a game da rashin daidaton da ake fama da shi a dangantakar tattalin arziki ta kasa da kasa, misali gibin cinikin Amurka a dangantakarta da China. Wajibi ne a tsayar da wata ka’ida da ta shafi jin dadin rayuwar jama’a a wannan hulda. Misali akwai mummunan gibi tsakanin kasashen Turai da Amurka a bangare guda da kuma China da Indiya a daya bangaren. Misali maganar kare hakkin mawallafa da kirkire-kirkire da China ke sako-sako da ita zata samu shiga a zauren taron kolin na kasashen G8 a shekara mai zuwa idan Allah Ya kai mu. Sai kuma maganar makamashi. A nan ma za a ba da la’akari da yunwar makamashin da kasashen Indiya da China ke yi a halin yanzu haka. Wadannan bayanan dai na masu yin nuni ne da cewar taron kolin zai mayar da hankalinsa akan wasu kasashe wadanda ba zasu halarci zauren ba. A sakamakon haka Ulrich Wilhelm yake cewar:

“Gwamnatin Jamus na fatan ba da sabon jini wajen tafiyar da dangantakar tattalin arzikin ta kasa da kasa a karkashin wani kyakkyawan yanayi mai gamsarwa kuma a halin yanzu haka ta fara shirye-shiryen tattaunawa da tuntubar juna tare da gaggan kasashe biyar dake da matsakaicin ci gaban masana’antu, wadanda suka hada da China da Indiya da Brazil da Mexiko da kuma Afurka ta Kudu.”

Gwamnatin Jamus ta yi fatali da bukatar da kasashen China da Indiya suka gabatar a game da shiga inuwar gamayyar ta G8, duk kuwa da cewar a a fakaice da yawa daga jami’an siyasar kasar sun hakikance cewar a halin yanzu haka rawar da kasar China ke takawa a tattalin arzikin duniya tuni za zarce ta kasashen Italiya da Spain dake da wakilci a gamayyar. Magana ta biyu kuwa kamar yadda aka yi bayani tun farko ta shafi raya makomar kasashen Afurka ne kuma za a gayyaci wakilan wasu daga cikin kasashen zuwa zauren taron domin musayar ra’ayi akan yadda za a tinkari matsalolin dake addabar nahiyar kamar dai cutar nan ta kanjamau dake nema ta zama gagara-badau. A kafada-da-kafada da wannan taron gwamnati a fadar mulki ta Berlin na shawarar kiran wani babban taro akan al’amuran Afurka shekara mai zuwa.