1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus zata ta ka rawar gani wajen warware rikicin Iraki

December 9, 2006
https://p.dw.com/p/BuYk
A tattaunawar da ya yi da sakatariyar harkokin wajen Amurka C-Rice a birnin Washington, ministan harkokin wajen Jamus F-W Steinmeier ya tabo hanyoyin da za´a bi don warware rikicin kasar Iraqi. Dukkan mutanen biyu sun kuma yi musayar yawu dangane da shigar da Jamus a shawarwari na diplomasiya kamar yadda rahoton Baker da Hamilton ya ba da shawara. Mista Steinmeier ya ce ba a tsayar da shawara akan wannan batu tukuna ba. Ya ce da farko dole sai gwamnatin Amurka ta shawarta game da matakan da zata dauka nan gaba a Iraqi. Sakatariyar harkokin wajen Amurka ta sake nuna adawa da yin shawarwari kai tsaye da Syria da kuma Iran. Ta ce dukkan kasashen biyu na marawa ayyukan ta´addanci baya. Ta kara da cewa kafin a yi haka dole sai Iran ta yi watsi da shirinta na nukiliya.