1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus zata taka rawar warware rikicin gabas ta tsakiya

Ibrahim SaniNovember 14, 2007
https://p.dw.com/p/CDql

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce da alama kwalliya zata biya kuɗin sabulu, a game da taron Yankin gabas ta tsakiya da Amirka ke shirin gudanarwa.Merkel ta faɗi hakanne dazu, jim Kaɗan bayan ganawarta da Sarki Abdallah na Saudiya. Shugabar Jamusawan tayi fatan cewa wannan taro, zai taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin yankin na gabas ta tsakiya, musanmamma a tsakanin Israela da Palasɗinawa.Angela Merkel ta kuma tabbatar da cewa Jamus zata taka muhimmiyar rawa, wajen ganin an cimma burin da aka sa a gaba.Tuni Sarki Abdallah ya yi maraba da wannan tayi na Jamus, da cewa yazo a dai dai lokacin da ake buƙatarsa.Shugabannin biyu dai sun tattauna halin da ake ciki a yankin na gabas ta tsakiya ne da kuma taron da Amirka zata gudanar, a game da rikicin yankin. Nan da wata ɗaya ko biyu ne Amirkan, ke shirin gudanar da wannan taro game da yankin na gabas ta tsakiya, a jihar Maryland dake Ƙasar.