1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamusawa biyu sun mutu a harin Masar

Mouhamadou Awal Balarabe
July 15, 2017

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta tabbatar da mutuwar 'yan kasarta biyu a harin da aka kai ranar Jumma'a a wurin shakatawa na bakin teku da ke Hourghada a gabashin Masar.

https://p.dw.com/p/2gadC
Ägypten Anschlag auf Polizisten
Hoto: picture-alliance/dpa/APA Images via ZUMA Wire/A. Sayed

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus  ta bayyana bakin cikinta a birnin Berlin dangane da amfani da wuka da wanda ya kai harin ya yi wajen kashe 'yan yawon shakatawa Jamusawa guda biyu. Dama dai mata biyu ne aka tabbatar da mutuwarsu a harin na Masar yayin da wasu karin hudu kuma suka samu raunuka.

Ko da shi ke dai an kama wanda ya kai harin, amma har yanzu ba a san musabbabin aikata wannan danyen aikin ba. Sannan ba wata kungiya da ta daukin alhakkinshi. Ita dai Masar ta saba fuskantar hare-hare a wurarenta na shakatawa inda na baya-bayan nan ya kasance na cikin Janairun 2016, inda Turawa 'yan yawon bude ido uku suka ji rauni a wani harin da aka kai musu da wukake.

Tun dai bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Morsi ta 'yan Uwa Musulmi a shekarar 2013 ne, Masar ke fama da hare-hare musamman ma kan sojoji a yankin Sinai.