1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamusawa na jefa ƙuri'a a yanki - mafi ƙarfin masana'antu a ƙasar

May 9, 2010

Jamusawa miliyan 3 da 3,000 ne ke ka'ɗa ƙuri'ar su a yankin North Reihn - Westphalia dake Jamus

https://p.dw.com/p/NJfs
Hoto: AP

A yau Lahadi ne al'ummar yankin North Reihn - Westephalia dake nan Jamus ke zuwa rumfunsan zaɓe domin jefa ƙuria'ar zaɓen mambobin majalisar dokokin yankin, wanda shi ne yankin daya fi yawan jama'a kuma ke da ƙarfin masana'antu a Jamus. Kimanin mutane miliyan 13 da dubu 300 ne suka cancanci ka'ɗa ƙuri'a a wannan zaɓen da ake ganin an gaggauta kiran yin sa ne, wanda kuma sakamakon sa ka iya yin ƙafar ungulu da ƙawancen ta jam'iyyar Christian Democrat ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke yi - idan har ƙawancen ya gaza samun rinjaye.

Frimiyan yankin na yanzu Yuergen Ruettgers, na ƙoƙarin kare ƙawancen dake tsakanin jsam'iyyun Christian Democrats (CDU) ne da kuma Liberal Free Democrats (FDP). Ita kuwa babbar mai ƙalubalantar sa Hannelore Krafts daga jam'iyar Social Democrats (SPD), tana so ne ta sake karɓar iko a yankin, wanda ya haɗar da Bochum - mai yawan masana'antu, da Gelsenkirchen, sai Dusseldorf da Kolon, yankunan da kuma jam'iyyar ta ce ta mamaye na tsawon shekaru 39. Jam'iyyar shugabar gwamnatin dai, na fuskantar barazanar gaza samun rinjaye saboda rashin goyon bayan Jamusawa ga tallafin tattalin arziƙin da Jamus za ta baiwa Girka, ko da shike kuma ana ganin batun manufar Ilimi da kasafin kuɗi ga ƙananan hukumomi za su taka rawa a sakamakon.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh