1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jan Egeland ya bukaci Majalisar Dinkin Dunia ta ƙara maida hankali wajen kare fara hulla a ƙasashen da a ke yaƙi

June 29, 2006
https://p.dw.com/p/BusK

Sakataran hukumar bada agaji ta Majalisar Ɗinkin Dunia Jan Egeland , ya buƙaci komitin Sulhu, ya ƙara ɗaukar matakan kare al´umomi fara hulla, a cikin yaƙe-yaƙen da ke ɓarkewa a wasu sassa na dunia.

Egeland yayi wannan huruci albarkacin wata mahaura kai tsaye, akan batun, da komitun sulhu ya tsara jiya laraba.

Duk da cewar an samu raguwar yan gudun hujira a dunia, akwai sauran rina kaba, wajen tabatar da kariya ga jama´ar da ba ta ci kasuwa ba, rufunna ke fada mata, a lokatan yaƙe -yaƙe a dunia.

Yauni ya rataya a kan Majalisar Ɗinkin Dunia, na kare rayukan jama´a,kamar yada ta bayana a cikin dokokin ta, inji Jan Egeland.

Jami´in ya bada missalai, da ƙasashen Irak, Sudan , Uganda, Somalia, Afghanistan, da Jamhuriya Demokradiyar Kongo, inda mutanen da ba su ji ba su gani ba, ke shan azaba a dalili da yaƙi, amma Majalisar Dinkin Dunia, ta kasa ɗaukar mattakai na zahiri, domin tabbatar da kariya a gare su.

Mattaki ƙwaƙƙwara na cimma wannan buri, inji Jan Egelend, shine na saka takukumi ga ƙasashe da abun ya shafa, da kuma kuma ƙara faɗaɗa yancin dakarun shiga tsakani, na Majalisar Dinkin Dunia.