1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janar David Petraeus na Amirka ya kama aiki a Iraƙi

February 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuS8

Hafsan sojin Amirka Janar David Petraeus ya karbi ragamar jagorancin dakarun Amirka a Iraqi. Babban aikin janar din mai shekaru 54 kuma sojin lema shi ne aiwatar da shirin shugaba GWB na maido da tsaro da kwanciyar hankali a birnin Bagadaza bayan an girke karin dakaru dubu 20. A lokacin da yake magana a gun wani bukin a sansanin sojin Amirka dake wajen babban birnin na Iraqi, janar Petraeus ya ce ko da yake akwai jan aiki a gaba amma ba zai gagara yi ba.

“Aikin mu a cikin watannin nan gaba shine taimakawa da aiki da dakarun Iraqi don inganta matakan tsaro, don gwmnatin Iraqi ta iya magance manyan matsalolin da take fuskanta. Ta haka kuma za´a inganta tattalin arziki da sauran muhimman ayyukan hidimomin da ake yiwa jama´a. Za´a cimma manufar da aka sa a gaba.”