1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janye yajin aikin ma'aikatan wutar lantarki a Nijeriya

August 26, 2010

Ma'aikatan wutar lantarki a Nijeriya sun yi gargaɗin sake shiga yajin aiki - idan ba a biya musu buƙatunsu ba

https://p.dw.com/p/OxAF
Hoto: AP

Ma'aikatan hukumar kula da harkokin wutar lantarki a Nijeriya sun janye yajin aikin su na yini ɗaya game da neman ƙarin albashi a wannan Alhamis ɗin a dai dai lokacin da shugaban ƙasar Dakta Goodluck Jonathan ya shirya ƙaddamar da sabuwar manufar sa ga sashen kula da harkokin wutar lantarkin. Ƙungiyar ma'aikatan hukumar ta janye yajin aikin ne biyo bayan kiraye - kirayen da wasu fitattun 'yan Nijeriya suka yi musu, kana da alƙawarin da hukumomin suka yi na cewar, za su biya musu buƙatun su.

Wani jami'in hukumar, wanda ya buƙaci a sakaya a sunan sa  ya ce, a cikin wata sanarwar da ke ɗauke da sa hanun babban sakataren ƙungiyar, Joseph Ajoero a safiyar yau Alhamis, ta umarci ɗaukacin ma'aikatan su koma bakin aikin su - ba tare da wani ɓata lokaci ba. Ya ce gwamnati ta amince ta biya su kashi 150 cikin 100 na albashin da suka nema, tare kuma da biyan su ariyas na watannin da suka gabata, farawa daga shekara ta 2003, kamar yadda ma'aikatan suka nema, amma ya yi gargaɗin cewar, suna sa ran samun kuɗin nan da mako mai kamawa, idan ba haka ba kuma su sake tsunduma cikin yajin aikin.

 A yau ne kuma, a Lagos, cibiyar kasuwancin Nijeriyar, shugaba Jonathan ke ƙaddamar da sabuwar manufar da ta shafi inganta samar da wutar lantarki a ƙasar, wadda ta kwashe tsawon shekaru tana fama da matsalar.    

Mawallafi: Saleh Umar saleh

Edita:      Zainab Mohammed