1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

300609 Irak US-Truppenabzug

June 30, 2009

Sojojin Amirka sun fara janyewa da garuruwa da biranen ƙasar Iraƙi

https://p.dw.com/p/IeOk
Dakarun tsaron Iraƙi ke bikin karɓar ragamar tsaron ƙasarsuHoto: AP

Sojojin ƙasar Amirka da suka shafe shekaru shida a ƙasar Iraƙi suka fara janyewa daga cikin biranen ƙasar, a wani mataki na janye ɗokacin sojojin na Amirka a ƙarshen shekara ta 2011 idan Allah Ya kaimu. Wannan mataki dai na ɗaya daga cikin yarjeniyoyin da aka cimma tsakanin hukumomin Iraƙi da na Amirka.

Tun a daren Litinin ne dai 'yan ƙasar ta Iraƙi suka rinka harba tartsatsin wuta a sararin samaniyar ƙasar tare da gudanar da shagulgula a tituna da sauran guraren shaƙatawa kuma yau Talata dai ranar hutu ce a ƙasar ta Iraƙi wadda kuma gwamnatin Nuru al-Maliki ta sanyawa sunan ranar samun 'yancin gashin kai daga sojojin na Amirka da suka mamaye ƙasar a shekara ta 2003 da sunan neman makamai masu guba da ta zargi gwamnatin marigayi Saddam Hussain da mallaka.

An dai gudanar da faretin sojojin na Iraƙi da na Amirka a babban sansanin sojin Amirkan da ya samu halartar jigajigan gwamnatoci da na sojin ƙasashen biyu. Da yake tsokaci game da janyewar sojojin na Amirka babban kwamandan sojin na Amirka a Iraƙi Janar Ray Odierno ya yi nuni da cewa

"Yau rana ce da Amirkawa suke miƙa ragamar tabbatar da tsaro ga dakarun ƙasar Iraƙi."

Miƙa ragamar harkokin tsaron Iraƙi da Amirkawan za su yi dai na cike da barazanar tsaro, kamar yadda aka fara gani tun kafin tafiya ta yi nisa, domin bayan hare haren da bama bamai irin na ƙunar baƙin wake da haifar da hasarar rayukan 'yan Iraƙin a cikin makwannin nan: Ko a jajibirin janyewar sojojin na Amirka, wasu sojojin Amirka huɗu, Allah bai nuna masu wannan rana ba, domin kuwa wani bam da ya tashi ya halaka su. Lamarin da kwamandan sojin na Amirka Janar Odierno ya ɗora akan wasu da ya ce 'yan tsuraru ne dake neman kawo ciƙas ga shirin janyewar dakarun na Amirka.

Ya ce: "Wannan aiki ne na wasu 'yan tsiraru dake neman suna, domin hana ruwa gudu, amma wannan ba zai hana mu ci-gaba da wannan tsari ba."

Tun kafin wannan rana ce dai aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin al'umar ta Iraƙi dake goyon bayan janyewar Amirkawan da kuma masu neman su ci-gaba da tsaya wa domin ƙarasa aikin da suka faro, wanda suke zargin Amirkan da haifarwa, kamar dai yadda ake samun rarrabuwar kawunan mahukunta a Amirkan game da wannan shirin janyewar sojojin da gwamnatin Barak Obama ta baiwa fifiko tun bayan da ta hau kan karagar mulki a farkon wannan shekara da muke ciki.

Paul Pillar, masanin harkokin ƙasar ta Iraƙi ne a jami'ar Georgetown kuma tsohon jami'in hukumar leƙen asiri ta CIA. Ya yi tsokaci a game da wannan mataki, inda yake mai cewar

Ya ce:"Daga yanzu Amirka ba zata gudanar da wani sintirin soji na kanta ba a titunan Iraƙi. Aikin da sojojin da suka rage za su yi, shine na ba da horo da shawarwari ga sojojin Iraƙi akan harkokin tsaro da alhakin tabbatar da tsaron ya koma hannun su."

A jawabin da ya gabatar ta gidan Talabijin ɗin ƙasar, domin bikin wannan rana, Firaministan na Iraki, Nuru al-Maliki ya tabbatar wa al'uman ƙasar cewar, dakarun ƙasar a shirye suke su tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al'umar ƙasar, tare kuma da gargaɗi ga masu neman ta da zaune tsaye da su shiga taitayin su.

Nuru al-Maliki, wanda ya yaba tare da godewa Amirka bisa rawar da ta taka wajen sake gina Iraƙin ya kuma bukaci 'yan ƙasar da su haɗa kai domin ci-gaba da kuma ɗorewar ƙasar ta Iraƙi. Duk da wannan janyewa da sojojin na Amirka suka yi a biranen Baghdaza da Kirkuk da Falluja da kuma Mossol, akwai sojojin Amirka dubu 133 da za su ci-gaba da kasancewa a cikin Iraƙin.

Mawallafa: Ralf Sina/Babangida Jibril

Edita: Mohammad Nasiru Awal