1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan ta sanarda janye sojojinta daga Iraqi

June 20, 2006
https://p.dw.com/p/ButE

Firaministan kasar Japan Junichiro Koizumi ya sanarda shirin janyewar sojojin Japan daga kasar Iraqi.

Wannan sanarwa tazo ne kwana guda bayan Firaministan Iraqi Nouri Al-Maliki yace dakarunsa sun shirya karbar harkokin tsaro a Muthanna,inda sojojin kawance da suka da sojin Japan suke.

Rahotanni sun baiyana cewa,zaa fara janyewar sojin Japan su 550 maiyuwa a cikin wannan wata.

Babu dai wani sojan Japan da aka kashe ko ya taba samun rauni a kasar ta Iraqi,sai dai kasashe makawabta da kuma yawancin yan kasar ta Japan sunyi suka da kasancewar sojin Japan a Iraqi.