1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

JAPAN ZATA TAIMAKAWA AFRIKA YAKI DA TALAUCI

Zainab A MohammadApril 22, 2005

Taron Kungiyar kasashen nahiyar Asia dana Afrika da aka kaddamar yau a birnin Bandung din Indonesia a yau Jummaa zai iya kasancewa wata kaface wa Japan na taka rawar gani wajen taimakawa kasashen Afrika fita daga kangin talauci dasuke fama dashi,wanda kuma a hannu guda zai iya taimaka mata cimma burinta na samun zaunannen kujera a komitin sulhu na.

https://p.dw.com/p/BvcL
Primier Junichiro Koizumi na Japan da Sakatare General na MDD Kofi Annan,a taron Asia da Afrika a Indonesia.
Primier Junichiro Koizumi na Japan da Sakatare General na MDD Kofi Annan,a taron Asia da Afrika a Indonesia.Hoto: AP

Prime minista Junichiro Koizumi na Japan wanda ke cikin mahalarta wannan taron na yini biyu ,anasaran zai gabatar da sabon shiri na ninka taimakon da kasarsa take bawa Afrika na kimanin dalan Amurka Million dari biyar da ishirin da tara da dubu dari tara,daga cikin adadin agajin datakeyiwa kasahen ketare.

Ana saran wannan tallafi zai taimakawa harkokin noma,tabbatar da zaman lafiya da tallafawa masu masanaantu na kansu,inji majiyoyin kafofin yada labaru na Japan.

Yuichi Oba ,jamii a sashin Afrika na maaikatar harkokin wajen kasar yace,Japan zata duka tukuru wajen rage talauci a nahiyar Afrika,ta hanyar karfafa dangantakar cinikayya da nahiyar Asia.Wannan dai na mai zama wada babbar dama wa Japan.

Shekaru 50 da suka gabata,shugabannin kasashen Asia dana afrika 29 ne suka bayyana a birnin Bandung inda cikin farin ciki da alfahari suka kulla wannan dangantaka da nufin kare rarrabuwa sakamakon yakin duniya,da kuma kalubalantar matsayin da kasashen yammaci suka dauka na mamaye komai.Taron na wannan lokaci wanda ya samu halartan kasashen Afrika da suka samu yancin mulkin kai daga mulkin mallaka da danniya na kasashen yammaci,ya kasance wata dama cewa wa nahiyoyin biyu na mikewa tsaye domin neman yancin kansu,kuma sun samu,inji rahotannin jaridun Indonesia.

Duk dacewa kungiyar ta samu karuwan wakilai na kasashe sama da 100 a halin yanzu haka,har yanzu tana fama da watta babbar abokiyar gaba watau Talauci,matsalar da kasashe da dama musamman na Afrika suka kasa shawo kanta,duk da nasaran samun yancin kai.

A dangane da hakane Japan ke ganin cewa wannan wata kafa ce da zata taimakawa wadannan kasashe.Tokyo dai tana da nata manufa da wannan agaji da zata bayar,wannan manufa nata kuwa shine nekan kujera na dindindin a komitin sulhu na mdd,idan kuwa har ta cimma burinta wajen kauda talauci wa waddannan kasashe,to babu shakka ta cancanci sakayya da wannan kujera a mdd.

Tatuo Hayashi wanda ke jagorantar wata kungiya mai zaman kanta na Afrika na mai raayin cewa taron na Bandung zai samar da karin hanyoyi na dangantaka tsakanin Asia da Afrika musamman da kananan maaikata.A dangane da hakane Mr Hayashi ta wasu Kwararru ta fannin Afrika sukayi kira ga Japan data iNganta wannan tallafi datake bawa kasashen Afrika,fiyeda yadda ake kyautata zato.Kazalika sun kuma sanar da kaddamar da wani shirin tallafi na hadin Gwiwa tsakanin Japan wa Amurka,a karkashin jagorancin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu.

To sai dai banan gizo ke sakar ba inji Prof.Minoru Obayashi ,masani kann harkoki na tattali a hukumar kasa da kasa na tallafawa Afrika dake Japan,domin kowane irin yunkuri zaayi na tsamo Afrika daga kangin talauci na iya cin tura ,saboda dogon tarin rashin ingantattun gwamnatoci,da zasu lura da shirin.Amma yace bincike da suka gudanar na nuni dacewa akwai mutane masu basira,adalci da gasiya wadanda zaa iya kashe waddannan kudade akansu ,fiye da Jamian gwamnati.

A yan shekaru da suka gabata dai akwai ingantuwa ta fannin kayyakin da ake sarrafawa a Afrika zuwa kasuwannin Japan,kuma manazarta da kwararru na ganin cewa wannan taro na Bandun damace wa Japan na inganta dankon zumunci da Afrika.Wanda kuma a hannu guda zai jagoranci burinta na neman zaunanniyar kujera a MDD.