1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Afirka ta Kudu da rikicin Kwango

Mohammad Nasiru Awal AS
March 2, 2018

Nadin sabbin ministoci a Afirka ta Kudu da fargabar barkewar yaki a Kwango da rikicin Sudan ta Kudu sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/2tbH8
Südafrika - neuer Präsident Cyril Ramaphosa
Hoto: Getty Images/AFP/M. Hutchings

Za mu fara sharhi da labaran jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta yi tsokaci kan sabbin ministocin da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya nada, wanda muhimmai daga cikin mukaman aka ba wa masu sukar lamirin tsohon shugaban kasa Jacob Zuma.

Jaridar ta ce kwanaki 11 bayan rantsar da shi sabon shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya aiwatar da sauye-sauye wanda muhimmi daga cikinsu shi ne na mukamin ministan kudi, inda ya sake mayar da tsohon ministan kudi Nhlanhla Nene kan mukamin. Fiye da shekaru biyu da suka wuce tsohon Shugaban kasa Zuma ya sallami ministan saboda sukar wasu shirye-shirye na shugaban ciki har da shirin nukiliyar, sannan ya sanar da matakin tsuke bakin aljihu. Wani tsohon ministan kudin da shi ma Zuma ya kora wato Gordhan Pravin ya koma bakin aiki a matsayin mai kula da kamfanonin gwamnati 300 ciki har da kamfanin zirga-zirgar jiragen saman kasar ta Afirka ta Kudu da kamfanin samar da makamashi na Eskom. Jaridar ta ce a sane Ramaphosa ya kafa majalisar ministoci don daidaita al'amura da samun canji mai ma'ana.

Gargadi game da barkewar yaki a Kwango

Daga batun siyasar Afirka ta Kudu sai wani rikicin a kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango inda jaridar Berliner Zeitung ta ruwaito masana na gargadi game da yiwuwar barkewar yaki a kasar tana mai nuni da rigingimu da ake samu a yankuna da dama na kasar.

Proteste in Kinshasa Kongo
'Yan sandan Kwango na daukar matakan murkushe boren adawa da Shugaba KabilaHoto: Reuters/G. Tomasevic

Ta ce matakan murkushe zanga-zangar lumana ta adawa da Shugaba Joseph Kabila da jami'an tsaron kasar ke yi ya zama ruwan dare. A karshen mako ma an halaka mutane lokacin wata zanga-zanga da cocin Katholika ya kira. Rikicin na barazanar yaduwa da idan ba a yi hattara ba ka iya rikidewa zuwa wani yaki. Shi kuma Shugaba Kabila ya ki shirya sabon zabe tun bayan karshen wa'adin mulkinsa shekaru biyu da suka wuce. Kana ya yi fatali da yarjejeniyar da cocin ya shiga tsakani aka kulla don gudanar da zabe a karshen 2017. Watakila dalilin da ya sa shugaban mai shekaru 46 ke jan kafa shi ne wani sakamakon jin ra'ayi ya nuna cewa shugaban ka iya shan mummunan kaye a zabe.

Ga yunwa ga ta'asar jami'an tsaro

Har yanzu muna kan labari da ya shafi Kwango amma a kasar Ruwanda inda jaridar Die Tageszeitung ta ce wata zanga-zangar da aka fara don adawa da karancin kayan abinci ta kare da asarar rayuka. Jaridar ta ce har yanzu dai ba a san munin kisan gillan da 'yan sandar Ruwanda suka aikata ba, lokacin da suka bude wuta a kan 'yan gudun hijirar Kwango da suka kwashe kwanaki uku suna zanga-zanga a ranar 22 ga watan Fabrairu. 'Yan sanda sun ce mutum biyar suka mutu amma majiyoyi a yankin sun ce yawansu ya kai mutum 22. Jaridar ta ce lamarin ya nuna tabarbarewar mawuyacin halin da 'yan gudun hijira ke ciki a yankin Great Lakes.

Hatsarin fadawa sabon bala'i

Südsudan Soldaten der Opposition
Sojojin adawa a lardin Ayod a daidai lokacin da Sudan ta Kudu ke ci gaba da yakin basasaHoto: picture-alliance/AP Photo/S.Mednick

Sudan ta Kudu na fuskantar barazanar fadawa sabon bala'i, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai cewa aikata laifukan yaki da yunwa sun zama ruwan dare a kasar.

Ta ce tun wasu shekaru labarai marasa dadin ji ke fitowa daga Sudan ta Kudu inda yaki da rikice-rikice da yunwa suka zama ruwan dare a kasar wadda nan gaba kadan za ta cika shekaru bakwai da samun 'yancin kai. Duk fatan da aka yi na samun bunkasa da kwanciyar hankali bayan samun 'yancin yanzu dai ya kau sakamakon rikicin siyasar da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar.