1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Afirka sun yi kira ga Jammeh ya nuna dattako

December 16, 2016

Kungiyar raya kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta jaddada bukatar Jammeh ya sauka ya mika mulki cikin lumana bayan da sauya matsayin kin amincewa da sakamakon zabe.

https://p.dw.com/p/2UQIe
Gambia Staatskrise ECOWAS Treffen  Yahya Jammeh empfängt Delegation West-Afrikanischer Führer
Hoto: Reuters

A sharhin da ta rubuta mai taken dambarwar zaben shugaban kasa a Gambiya.Jaridar Zeuddeutsche Zeitung ta ce lamuran da suka biyo bayan sakamakon zaben sun kasance masu rikitarwa da sanya fargaba a zukatan al'umma bayan da ya sauya matsayi na kim amincewa da sakamakon zaben daya yarda da shi tun da farko.


Jaridar ta ce abin da ke da daure kai shine kwanaki takwas bayan zaben Jammeh ya sauya matsayinsa inda ya shaidawa taron manema labarai cewa bai amince da sakamakon ba, zai bukaci sake gudanar da wani sabon zabi karkashin wata sabuwar hukumar zabe mai adalci da tsoron Allah.

Yahya Jammeh
Hoto: AP

Wannan mataki a cewar Jaridar ya jawo martani daga sassa daban daban na duniya. Yayin da Amirka ta baiyana cewa matakin ko kadan ba za a amince da shi ba, shugaban hukumar tarayyar Afirka Nkosazana Dilamini Zuma watsi ta yi da maganar ta na mai cewa Al'ummar Gambiya sun riga sun bayyana zabinsu.

Kiran da kungiyar raya cigaban kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta yi wadda ta tura tawaga mai karfi ta kunshi shugabanin Najeriya da Ghana da Liberiya da kuma Saliyo zuwa Gambiya domin shawo kan Yahya Jammeh ya martaba zabin al'umma ya mika mulki cikin lumana ga mutumin da Allah ya baiwa nasara ga alama ba ta shiga kunnensa ba inda jam'iyyarsa ta shigar da kara a kotu tana kalubalantar sakamakon zaben.

Jaridar ta ce bayanin babban hafsan sojin kasar cewa yana aiki ne karkashin gwamnatin Jammeh kuma hakkinsa ne ya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gambiya ya nuna sojojin suna goyon bayan Jammeh.

Hannunka mai sanda ga Shugaba Kabila

Joseph Kabila Präsident Demokratische Republik Kongo
Hoto: Getty Images/AFP/T. Mianken

Jaridar die Tageszeitung a sharhinta, nuni ta yi ga alamar hannunka mai sanda da kungiyar tarayyar Turai ta yi wa shugaban Kongo Joseph Kabila wanda ministocin harkokin waje na kungiyar EU suka yi a makon da ya wuce kan aniyar tazarce a wa'adin mulkinsa da zai kare a ranar 19 ga wannan watan na Disamba. Kungiyar tarayyar Turan ta sanyawa wasu manyan shugabanni bakwai na hukumomin tsaron Kongo takunkumi da suka hada da rike kadarorin da suka mallaka da hana su zirga zirga a cikin kasashen Turai.

Ko baya ga wannan jaridar ta ce kasar Amirka ma ta tsaurara takunkumi akan shugabanin na Kongo da ya hada da haramta musayar kudade da dalar Amirka tsakanin bankuna a asusunsu na ajiya, matakin da zai yi tarnaki ga hamshakan attajirai na kasar.

Kawancen Turai da Afirka kan 'yan gudun hijira

Niger Binnenflüchtlinge Flüchtlinge Vertriebene Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Abodou

A mataki irinsa na farko na dakile kwarar yan gudun hijirar daga Afirka, jaridar Tageszeitung ta ce kungiyar EU na shirin kammala wata yarjejeniya da kasar Mali bugu da kari da bada karin gudunmawa ga kasar Niger kamar yadda ta cimma yarjejeniya da Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier.

Steinmeier ya shaidawa taron ministocin kungiyar tarayyar Turan a Brussels cewa ana da kwakwarar kudiri da gwamnatin Niger ba ma kan dakile kwararar yan gudun hijira ba kadai har ma da taimakawa gwamnatin sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na inganta ilmin yaya mata.

Jaridar ta Tageszeitung ta ce babbar nasarar manufofin kungiyar tarayyar Turai ba ta tsaya ga Niger kadai ba harma da Mali inda kungiyar tarayyar Turan ke taimakawa yaki da ta'addanci.