1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Harin ta'addanci a Bosso dab da kama azumi

Mohammad Nasiru AwalJune 10, 2016

Hare-haren Boko Haram a Bosso da ke Nijar da shirin aikin gina katafaren hanya a Najeriya da kokarin EU na dakile kwararar bakin haure daga Afirka.

https://p.dw.com/p/1J4R3
Niger Soldaten in Bosso
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Za mu fara labaran da sharhin jaridun Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Die Tageszeitung wadda ta ce a daidai lokacin da ake shirye-shiryen fara azumin watan Ramadan kungiyar Boko Haram ta kai mummunan hari a Nijar.

Jaridar ta ce harin da ke zama irinsa mafi muni da 'yan ta'addar daga Najeriya suka kai a garin Bosso da ke a Nijar ya girgizar wannan yanki na kan iyaka, da alkalumman hukuma suka ce sojoji kusan 30 aka kashe, sannan su kuma 'yan tarzomar sun rasa mutane da yawan gaske. Wannan lamarin ya dauki sabon salo tun a cikin watan Afrilu, inda Boko Haram ke yawaita kai hare-haren a tsallaken iyaka, a karshen watan Mayu da ya gabata ma ta hallaka mutane shida a yankin. Jihar Diffa wadda garin na Bosso ke cikinta ta dauki 'yan gudun hijira kimanin dubu 82 daga Najeriya, wadanda suka tsere daga ta'asar Boko Haram. Yanzu mazauna kauyuka na tserewa daga yankin na kan iyaka da Najeriya lamarin da zai kara jefa rayuwar mutane cikin tsaka mai wuya.

Aikin gina babbar hanya a Najeriya da muhalli

Daga Nijar bari mu garzaya Najeriya inda jaridar Neues Deutschland ta buga labari mai taken aikin gina wata babbar hanya na barazana ga muhalli.

Nigeria Proteste gegen Straßenbau in Ekuri
Ana rufa-rufa inji Odigha Odigha tsohon shugaban hukumar gandun dajin Cross River da ke adawa da aikin gina hanyarHoto: DW/A. Kriesch

Ta ce shirin gina wata babbar hanya da ake takaddama kai ka iya lalata dajin kurmin jihar Cross River. Aikin zai kuma kasance wani mataki da ya saba wa yarjejeniyar kasa da kasa na kare dazuzzuka. Ita ma kanta gwamnatin Najeriya na fama da rarrabuwar kai game da aikin. Jaridar ta ce katafaren aikin gina sabuwar hanyar mai tsawon kilomita 260 zai ratsa gandun dajin kasa da ke yankin Ekuri na jihar Cross River, yankin da ke zama wani bangare na aikin Majalisar dinkin Duniya na kare dazuzzuka da dabbobin dawa da sauran halittun da ke ciki.

Taimako ko jan kunne

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung a wannan makon tsokaci ta yi kan matakin kungiyar Tarayyar Turai na yi wa manufofinta na hijira kwaskwarima inda za ta hada kai da wasu kasashen Afirka don dakile kwararar bakin haure daga Afirka zuwa Turai.

Libyen Flüchtlinge aus Afrika auf dem Weg nach Europa verhaftet
'Yan gudun hijira daga Afirka da ke kokarin shiga Turai daga kasar LibyaHoto: picture-alliance/AA/H. Turkia

Jaridar ta ce tun farko Tarayyar Turai ta nuna karara cewa za ta tilasta wa Afirka aiki da ka'idojin yarjejeniyar domin ba ta ba su zabi ba. Kungiyar EU din dai ta ce za ta saka wa kasashen Afirka da suka ba ta hadin kai a shirin na mayar da bakin haure ta hanyar ba su taimakon raya kasa da saukaka musu hanyoyin yin hulda ciniki da Turai, amma wadanda suka nuna taurin kai za su dandanin kudarsu, domin ana iya sanya musu takunkumai ciki har da na tattalin arziki da ciniki.

Rigingimu na barazana ga kasar Mozambik

A karshe sai jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka kasar Mozambik tana mai cewa har yanzu ana fama da rashin tsaro a wasu yankuna na kasar Mozambik, dalili kuwa shi ne tsoffin 'yan tawaye na cigaba da fada. Ta ce a wasu shekaru kalilan da suka wuce Mozambik ta zama wata kasa mai cike da kyakkyawan fata biyo bayan gano arzikin mai da iskar gas, da aka sa rai zai habbaka tattalin arzikinta, amma kash, yawan fada yanzu tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye na yin tuni da yakin basasan da kasar ta yi fama da shi tsakanin 1975 da 1992 da ya yi sanadin salwantar rayuka miliyan daya.