1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus kan Afurka

Lawal, TijaniFebruary 1, 2008

Sharhunan Jaridun Jamus kan Lamuran Afurka a Wannan makon

https://p.dw.com/p/D19j
Omar Bongo da Metasebia TadessaHoto: AP


AU/Nigeria/Tchad/Niger


A wannan makon jaridun na Jamus sun yi bitar matsaloli iri daban-dabam dake addabar nahiyar Afurka, suna masu ba da la'akari da taron kolin shuagabannin kasashen kungiyar tarayyar afurka da aka gabatar a birnin Addis Ababa a tsakiyar mako. Amma da farko zamu fara ne da duba wani dogon sharhi da mujallar Der Spiegel ta gabatar a kan matsalar magunguna na jabu, wadanda ta ce a halin yanzun Nijeriya tafi kowace kasa yin kaurin suna a wannan matsala, inda ita kanta shugabar hukumar kiwon lafiya ta kasar take fuskantar barazana game da makomar rayuwarta a kokarinta na yaki da matsalar ta sarrafa magunguna na jabu. Mujallar ta kara da cewar:


Nigeria

"Dora Akunyili dake da shekaru 53 da haifuwa tana cikin hali ne na dardar game da rayuwarta, a matsayinta na shugabar hukumar kula da abinci da magunguna ta Nijeriya Nafdac a takaice. Domin kuwa a halin yanzu haka tana fafutukar saka kafar wando daya da masu sarrafa magunguna na jabu dake samun kazamar riba suna masu barazana ga makomar lafiyar mutane kimanin miliyan 140. Safarar wadannan m iyagun magunguna na jabu kan yi sanadiyyar rayukan dubban daruruwan mutane a sassa dabam-dabam na duniya, kuma Nijeriya na daya daga cikin manyan ummal'ba'isin wannan kazamar hada-hada mai samar da dubban miliyoyi na dalar Amurka."


AU

A wannan makon shuagabannin kasashen kungiyar tarayyar Afurka ta AU suka kaddamar da taron kolinsu a birnin Addis Ababa a karkashin taken makomar ci gaban masana'antu a nahiyar Afurka. A lokacin da take ba da rahoto akan wannan taro jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:


"Babban abin dake hana ruwa gudu wajen samun cikakkiyar kusantar juna tsakanin kasashen kungiyar tarayyar Afurka su 53 shi ne banbance-banbancen matsayinsu na ci gaba, musamman ma ganin yadda kasashe irinsu Somaliya da Kongo da Sudan da kuma Kenya a baya-bayan nan ke fama da rikici. Wannan matsalar ma ita ce ta fi daukar hankalin mahalarta taron kolin a maimakon ainihin taken da aka ba shi."


Niger

Ita ma kasar Nijer tana ci gaba da fama da zaman dardar a arewacinta sakamakon tawayen 'yan kabilar Tuarek. A lokacin da ta tabo wannan rikici, jaridar Neues Deutschland cewa tayi:


"Rikicin na Tuarek a arewacin Nijer na da nasaba ne da tattalin arziki sakamakon dimbim arzikin ma'adanin Uranium da Allah Ya fuwace wa yankin Arlit a hamadar Sahara, wanda kamfanin Areva na Faransa ke hakowa, kuma a halin yanzu haka Nijer ita ce ta biyu wajen cinikin Uranium a duk fadin duniya"

Tchad

A wannan makon ne kuma kungiyar tarayyar Turai ta fara tura sojojinta zuwa kasar Chadi domin taimakawa wajen kare makomar 'yan gudun hijira a gabacin kasar. Jaridar Berliner Zeitung tayi sharhi akan haka tana mai cewar:


"Amma fa ko da yake manufar kare makomar rayuwar farar fula ita ce hujjar da kungiyar tarayyar Turai ta bayar a game da tura dakarun nata su kimanin dubu 3 da 700 zuwa Chadi. To sai dai kuma a daya bangaren tayi bayanin barin babin katsalandan soja a lardin Darfur na kasar Sudan a bude, lamarin da ya sa ake tababa a game da ainfin makasudin wannan mataki. Ita dai Chadi tana daya daga cikin kasashe uku na nahiyar Afurka dake da muhimmanci matuka ainun ta fuskar tsaro, a baya ga Djibouti da Eritrea, wadanda ke kusa da mashigin tekun pasha. Ita kuwa Chadi tana makobtaka ne da Nijer, mai arzikin Uranium, sai kuma Nijeriya da Libiya da Sudan dake da dimbin arzikin man fetur. Wannan shi ne ainifin dalilin tura sojojin na kungiyar tarayyar Turai. Jaridar ta ce abin madalla shi ne yadda Jamus ta tubre ta ce faufau ba zata ba da gudummawar soja koda kwaya daya a wannan mataki ba."

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung tayi bitar batun inda take cewar:

"Ainifin nauyin da aka dora wa sojojin na Eufor a Cadi da Janhuriyar Afurka ta Tsakiya shi ne ba da kariya ga 'yan gudun hijira da share hanyar kai taimakon jinkai da tabbatar da cewar jami'an Majalisar Dinkin duniya sun samu isa wuraren da ake bukatar taimakonsu. Amma fa kasashen Jamus da Birtaniya na tababa a game da fa'idar wannan mataki, a saboda haka suka ki shiga a dama da su. Gaba daya kasashe 14 ne kacal daga cikin kasashe 27 na Kungiyar Tarayyar Turai ke da hannu a cikinsa."