1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: sanya dan kwali a Gambiya

Mouhamadou Awal BalarabeJanuary 8, 2016

Tilasta wa matan Gambiya Musulmi da Kiristoci lullube kawunansu a wurarensu na aiki da shugaban Gambiya Yahya Jammeh ya yi ya daukan hankali jaridun tarayyar Jamus.

https://p.dw.com/p/1Ha9V
Malta Flüchtlingszentrum Balzan in Valletta
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Kumm

A cikin sharhin da ta yi jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce dokar sanya dan kwali bayan ayyana Jamhuriyar Musulunci za ta iya gurganta kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin Musulmi da kuma Kiristocin kasar Gambiya. A cewarta dai shugaba Yahya Jammeh ya rikidar da kasar zuwa Jamhuriyar Musulunci ne domin ya dadada wa manyan kasashen yankin Golf tare da samun kundin shiga daga garesu, bayan da Kungiyar Gamayyar Turai ta katse duk wani tallafin da ta saba baiwa Gambiya.

Jaridar ta kara da cewar ba wani abin kirki da Yahya Jammeh ya yi tun bayan da ya dare kan kujerar mulki illa dada jefa kasar cikin mawuyacin hali. Majalisar Dinkin Duniya ta nunar da cewar kashi 70% na 'yan Gambiya na rayuwa cikin talauci. Sannan kuma gwamnatin kasar na daure duk masu adawa da manufofinta maimakon neman inganta halin rayuwar talakawa da kuma daidaita kawunanan Musulmi da kuma Kiristocin kasar ta Gambiya.

Nigeria Ölplattform vor der Küste
Hoto: AP

Wani karin batu da Jaridun Jamus suka yi tsokacin a kai shi ne halin rashin tabbas da tattalin arzikin ya samu kansa a ciki sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya. Wannan matakin dai ya sa gwamnatoci rage kudin da suke warewa a kasafin kundinsu don gudanar da ayyukan raya kasa.

Jaridar Tageszeitung ta nunar da cewar kasashen Afirka da suka dogara a kan fetur wajen samun kudin shiga, sun samu kansu ciki masassarar tattalin arziki saboda farashin gangan mai ya fadi da kashi 80% a cikin shekaru biyu na baya-bayannan. Wannan lamari dai ya dagula wa kasashe irinsu tarayyar Najeriya da kuma Angola lissafi saboda kudin da ya shiga aljuhunsu ba kai rabin abin da suka yi hasashe da farko ba.

Tgeszeitung ta ce wannan matsalar farashin man ya sa gwamnatocin kasashen Afirka tsuke bakin aljuhunsu a kasafin kudin wannan sabuwar shekara. Wannan ya na nufin cewar gine-ginen asibitoci da makarantu da hanyoyin za su ja baya, lamarin da zai sake mayar da hannu agogo baya a kokarin inganta halin rayuwar talakawan Afirka.

Tierärzte Ohne Grenzen
Hoto: Florian Schuh

Bari mu karkare da sharhin da Süddeutsche Zeitung ta yi a kan rikicin da dabobbi ke haddasawa tsakanin manoma da makiyaya ko maharba a nahiyar Afirka. Jaridar ta ce a wasu kasashe za a iya kawo karshen kashe karkanda da giwaye da ake yi domin sayar da haurensu. Sai dai kuma ba zai yi wa manoman wasu kasashen nahiyar Afirka dadi ba saboda dabbobin na lalata musu amfanin gona tare da hadassa fadace-fadce tsakaninsu da maharba.

Sai dai kuma jaridar ta ce wannan zai iya zama tarihi idan aka yi amfani da tsarin da aka girka a kasashen Botswana da kuma Kenya, inda manoma suke nomar zuma a kewayen gonakinsu da nufin hana dabbobi lalata musu amfanin gona.