1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Shari'ar Gbagbo a kotun ICC

Mohammad Nasiru AwalJanuary 29, 2016

Shari'ar da kotun duniya ke wa tsohon shugaban Cote d'Ivoire da siyasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/1Hls1
Elfenbeinküste Präsident Laurent Gbagbo
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kooren

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus kan nahiyar Afirka da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta buga labari kan shari'ar da ake wa tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo a kotun kasa da kasa ta ICC da ke birnin The Hague. Jaridar ta bayyana shari'a da ta tarihi. Kotun dai na zargin Gbagbo da tsohon ministansa Charles Blé Goudé da aikata laifi kan dan Adam a rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar ta Cote d'Ivoire a karshen shekarar 2010. A farkon zaman shari'ar a ranar Alhamis mutanen biyu ba su amsa lafin da ake zarginsu da aikatawa ba. Masharhanta dai sun ce za a iya daukan tsawon shekaru hudu ana wannan shari'a.

Zagaye na biyu na zaben Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

A labarin da ta buga game da zaben na Jamhuriya Afirka ta Tsakiya jaridar Die Tageszeitung ta fara ne da cewa sakamakon zabe da ya zo da mamaki ya tilasta zuwa zagaye na biyu.

Zentralafrikanische Republik Bangui Wahlen Wahllokal
Hoto: picture-alliance/AP Photo/H. Diaspora

Tun bayan da kasar ta fada cikin rikici kimanin shekaru uku da suka wuce babu ko daya daga cikin 'yan siyasar da ke neman shugabancin kasar yanzu da ya yi wani abin kirki. Yanzu dai mutane biyu ne daga cikin 'yan takara 30 da suka shiga zaben shugaban kasar na ranar 30 ga watan Disamban 2015, za su fafata a zagaye na biyu, sauran kuwa sun bace daga fagebn siyasar kasar. Sai a ranar 25 ga watan nan na Janeru kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da sunayen mutane biyun da suka cancanci zuwa zagaye na biyu. Wanda ya zo na farko shi ne Anicet-Georges Dologuélé tsohon shugaban babban bankin kasar, da Faustin-Archange Touadéra, Firaministan karshe a mulkin Francoiss Bozizé a matsayi na biyu.

Ita ma a sharhin da ta yi game da zaben jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi tsoffin 'yan gatar kasar ne suka mamaye zaben. Sai dai ta ce wani albishir daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai fama da yakin basasa shi ne nan gaba kadan za ta samu sabon shugaban kasa. Yanzu haka dai a zagaye na biyu na zaben da zai gudana ranar 7 ga watan Fabrairu, za a fafata ne tsakanin Anicet-Georges Dologuélé da Faustin-Archange Touadéra dukkansu biyu tsoffin Firaministoci.

Tallafin kudin karatu ga wadda ta kare budurcinta

Kopftuch in Südafrika
Hoto: DW/S. Govender

A wannan makon jaridar Berliner Zeitung ta leka wani lardi ne da ke kasar Afirka ta Kudu tana mai cewa tallafin kudin karatu ga 'yan mata da suka kare budurcinsu. Ta ce shugabannin a lardin Kwa-Zulu/Natal a kasar Afirka ta Kudu sun yanke shawarar tallafa wa 'yan matan da suka kare budurcinsu da kudin karatu a jami'a. Yanzu haka dai wasu 'yan mata 16 'ya'yan marasa galihu ne za su fara cin gajiyar wannan shiri, bayan da aka tabbatar cewa ba su san maza ba. Dalilin wannan mataki shi ne yankin na daga cikin wurare a Afirka ta Kudu da suka fi yawan masu dauke da kwayoyin cutar HIV-Aids ko Sida. Hakazalika suna da mafi yawan 'yan matan da ke katse karatun boko saboda daukar ciki. Saboda haka aka dauki wanna matakin saka wa budurwar da ta mayar da hankali kan neman ilimi.