1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Zabubbuka a kasashe da dama na Afirka

Umaru AliyuMarch 25, 2016

Zabubbukan gama gari da aka gudanar a kasashen Afirka da dama ciki har da Nijar da Benin sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/1IJwu
Niger Wahl Wähler in Niamey
Hoto: DW/A. Amadou

Jaridun na Jamus da dama sun yi sharhi game da zabubbukan shugaban kasa da aka yi a kasashe shidda a karshen makon jiya, inda masu zabe suka kada kuri'unsu a kasashen Jamhuriyar Nijar, Kwango Brazzaville, Jamhuriyar Benin, Cape Verde da Zanzibar da kuma zaben jin ra'ayin jama'a kan kundin tsarin mulki a Senegal.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta tabo nasarar da shugaban Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou ya samu, inda ta ce wannan nasara ce da idan ba a yi hankali ba za ta iya jefa kasar cikin rudami. A wannan zabe shugaban mai ci ya sami kashi 92.5 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da abokin takararsa Hama Amadou ya tashi da misalin kashi 7.5 cikin 100. Nasarar Mahamadou Issoufou ta zo ne daidai lokacin da dan takara Hama Amadou yake Faransa don neman magani, bayan wata da watanni da yayi a tsare a gidan kaso. Nijar, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana cikin kasashen da ke fuskantar barazanar aiyukan 'yan tarzoma, ganin makwabatanta da kasashe kamar Mali da Burkina Faso da Najeriya, wadanda gaba daya kungiyoyin musulmi masu matsanancin ra'ayi suka tasa su gaba.

Hukunci kan laifin aikata rashin imani

Niederlande Den Haag ehemaliger Vizepresident Kongos
Jean-Pierre Bemba a gaban kotun duniya da ke The HagueHoto: picture-alliance/AP Images/J. Lampen

Jaridar Süddeutsche Zeitung Zeitung ta yi sharhi game da hukuncin da kotun kasa da kasa da ke birnin The Hague ta yanke wa tsohon shugaban 'yan tawayen Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, Jean-Pierre Bemba, wanda aka same shi da laifin aiyukan rashin imani, kashe-kashe da fyade a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wadanda suka gabatar da shi a kotun sun zargi Bemba da laifukan yaki, wadanda mayakansa suka aikata tsakanin shekara ta 2002 zuwa 2003. Tsohon dan tawayen an same shi da laifin bai wa magoya bayansa 'yan kungiyar neman 'yanci ta Kwango, wato MLC, damar azabtar da dimbin mutane maza da mata da yara a makwabciyar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Shari'ar a kotun kasa da kasa ita ce irinta ta farko da aka dora ta kan laifukan da suka shafi fyade a matsayin wani makami da 'yan tawayen suka yi amfani da shi.

Tsallake rijiya da baya kan wata badakala

Ausschnitt Jacob Zuma in Burundi
Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta KuduHoto: Reuters/E. Ngendakumana

Jaridar Berliner Zeitung ta tabo halin da ake ciki ne a Afirka ta Kudu, inda shugaban kasa Jacob Zuma ya sake tsunduma cikin wani abin kunyar, a wannan karo, tattare da dangantakarsa da iyalin Gupta 'yan kasuwa kuma masu masana'antu a kasar. Sai dai jaridar ta ce a wannan karo ma, kamar a lokutan baya, Zuma ya sake tsallake rijiya da baya tattare da wannan abin kunya, saboda majalisar shawara ta kololuwa a kasar ta kammala taronta ba tare da an yanke wani kudiri game da makomar Zuma kan wannan abin kunya ba. Shugaban na Afirka ta Kudu ana zarginsa ne da kasancewa dan amshin shatan iyalin na Gupta, wadanda ya kyale suna ta aiyukan cin rashawa ba tare da an tsawatar masu ba.

Matsalar kamfar ruwa a Afirka

A karshe, cikin wani sharhi da ta yi, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta duba halin karancin ruwan sama da yiwuwar fuskantar yunwa a nahiyar Afirka. Jaridar ta ce a yankunan Somaliya da wasu kasashe na Afirka da dama, yanzu haka yunwa na neman zama bala'i, sakamakon rashin ruwan sama. Wannan kuwa ya biyo bayan canji ne na yanayi da ke samuwa daga El Nino. Wadannan yankuna da ke fama da matsalar fari ko yunwa, ba sa kuma samun wani taimako daga ko ina, ko dai saboda matsalar siyasa ko kuma rashin yadda za a iya kai masu taimakon.