1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun sun fi mayar da hankali ne akan rikicin Somalia

Mohammad Nasiru AwalJanuary 12, 2007

Harin da Amirka ta kai a kudancin Somalia ya kara jefa al´umar Somalia cikin rudu game da makomar kasar su.

https://p.dw.com/p/BvPR
Sojojin Somalia da Habasha a Kismayo
Sojojin Somalia da Habasha a KismayoHoto: picture-alliance/ dpa

To a wannan makon jaridun na Jamus sun mayar da hankali ne akan rikicin kasar Somalia, musamman dangane da harin da Amirka ta kaiwa a kudancin kasar ztana mai farautar wasu ´yan al´Qaida.

A sharhin da ta rubuta jaridar FAZ ta ce harin da Amirka kai a Somalia kan wadanda ta ke zargi ´ya´yan al-Qaida ne ya nunar a fili yadda gwamnati a Washington ke daukar barazanar ayyukan ta´adanci, wadda alal hakika ita ce ke janyowa kanta. Jaridar ta ce Somalia ta kasance kasar da yaki ya yiwa kaca-kaca wadda ba zata iya kare kanta daga ´yan ta´adda ba kuma ba ta canza zani ba duk da nasarar da aka samu kan ´yan Islama tare da taimakon dakarun Ethiopia. Da farko Amirka ta yi ikirarin kashe wani kusa na al-Qaida a wannan hari to amma ka da ta manta cewa sai da ta salwantar da rayukan bayin Allah wadanda ba su san hawa ba su san sauka ba. Ita kuwa jaridar TAZ a sharhin ta cewa ta yi hmm abin mamaki shugaba Abdullahi Yusuf bai damu ba da hare haren da Amirka ke kaiwa kasarsa. Duk da asarar rayuka da harin ya janyo, shugaban ya fadawa wani taron manema labarai cewa Amirkawa ba su yiwa al´umarsa wani ta´adi ba, illa iyaka yaki suke yi da ´yan ta´adda na Somalia da na kasa da kasa. Jaridar ta ce kamata yayi a fara duba hanyoyin samar da zaman lafiya a Somalia maimakon sake saka kasar cikin wani mawuyacin hali tare da hannun manyan daulolin duniya. A wani labari da ta rubuta jaridar SZ cewa ta yi yaki da ta´addanci da yanzu Amirka ta kaddamar a Somalia babu abin da ya janyo sai karin magoya baya ga masu kishin Islama. Jaridar ta ce wannan mataki da Amirka ta dauka ba komai ba ne illa kawai ta na son ta nunawa duniya ne cewar ba ta yi kasa a guiwa ba a matsayin ta na babbar daula. Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubata sharhi akan mawuyacin hali da al´umar kasar Somalia ke ciki sakamakon yakin basasan na shekaru 15. Jaridar ta ce a cikin wadannan shekarun da yawa daga kungiyoyin agaji masu zaman kansu sun fice daga wannan kasa saboda dalilai na rashin tsaro. Amma Kungiyar agaji ta likitoci wato Medicines Sans Frontiers na daga cikin ´yan agaji kalilan da suka saura a Somalia. Jaridar ta ce wannan hali da aka shiga na rashin sanin tabbas a Mogadishu hade da harin da Amirka ta kaddamar akan Somalia ya sa ana kara saka ayar tambaya ko zaman lafiya zai samu a kasar bare a fara batun kai mata dauki.

Yanzu kuma sai zauren MDD inda babban sakataren majalisar Ban Ki Moon ya nada ministar harkokin wajen Tanzani Asha-Rose Migiro a mukamin mataimakiyar sa. A wani sharhi da ta rubuta jaridar SZ ta ce yanzu dai matsayin Dr. Migiro ya kai kololuwar sa a fagen siyasar duniya sakamakon wannan ci-gaba da ta samu. Dr. Migiro mai shekaru 50 kuma lauya ita ce zata jagoranci ayyukan yaki da talauci, yunwa da kuma rigingimu a madadin MDD. Jaridar ta ce ganin yadda nahiyar Afirka ke fama da wadannan matsalolin, to Dr. Migiro na da jan aiki a gabanta kuma ko shakka babu zata taka rawar gani don tallafawa nahiyarta fita daga cikin wannan kangi na wahalhalu. Ko da yake kawo yanzu ba ta bayyana manufofinta ba amma bisa ga dukkan alamu Migiro zata bawa hadin kan tattalin arziki tsakanin kasa da kasa muhimmanci. A binciken da ta yi lokacin da take karatun digirgir a jami´an Konstanz dake nan Jamus ta mayar da hankali kan hadin tattalin arziki a gabashi da kuma nahiyar Afirka. Hakazalika Migiro ta sha rubuta kasidu game da ´yancin mata, ´yancin ´yan jarida da kuma kaurar da ´yan Afirka ke yi zuwa Turai.

Yanzu kuma sharhin da jaridar Neues Deutschland ta rubuta game da zaman taro karo na biyu akan Afirka a birnin Accra ta kasar Ghana daga ranar 12 zuwa 14 ga wannan wata, wanda shugaban tarayyar Jamus ke halarta. Jaridar ta ce taron ya nunar a fili yadda shugaban na Jamus ke son a nunawa nahiyar Afirka adalci a huldodin cinikaiya tsakanin ta da kasashe masu arziki. Ta haka ne kadai Afirka zata iya dogaro da kanta maimakon kullum a rika ba ta taimakon raya kasa, wanda a karshe suke karewa a aljihun shugabannin ta.