1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

jawabin Bush game da iraqi da kuma kokarin ganin dimokradiyya ta wanzu ako, ina a duniya

ibrahim saniMay 19, 2005

Bush yace akwai matsala game da yakin iraqi

https://p.dw.com/p/Bvbq
Hoto: AP

Shugaba Bush na Amurka a karon farko a tun bayan hambare mulkin tsohon shugaban iraqi Saddam Hussain da kuma kafa sabuwar gwamnati a kasar,yace babu shakka Amurka na fuskantar matsala babba game da aniyar data sa a gaba na tabbatar da tsaro da oda a fadin kasar ta iraqi baki daya.

Shugaba Bush yaci gaba da cewa darasi da Amurka ta koyxa a yanzu haka daga yakin na iraqi shine kokarin daukar mataki daya dace bisa tsari da kuma aiwatar dashi yadda aka tsara shi.

A don haka a halin yanzu a cewar Bush Amurka zata dinga daukar matakai da suka dace cikin gaggawa don taimakawa kasashen dake son tabbatuwar mulkin dimokradiyya a cikin kasashen nasu ba tare da wani bata lokaci ba.

Bisa wan nan matsala da Amurkan ta fuskanta a cewar Shugaba Bush a yanzu haka akwai wani tanadi da gwamnatin sa tayi a cikin kasafin kudi na tanadin wasu jamiin masu kayan sarki,wadan da za a tura su duk inda ake wani rikici ko yaki na basasa don bayar da taimakon daya dace a kann lokaci.

Shugaban wanda yake fadin haka a lokacin da yake gabatar da jawabi a dakin taron wata cibiya ta republikan dake inganta tabbatuwar mulkin dimokradiyya a doron kasa yaci gaba da cewa a yanzu haka gwamnatin sa ta gabatar da bukatar ware dalar Amurka miliyan 100 don samar da wan nan tawaga ta jamiin sarkin a waje daya kuma da wata dalar miliyan 24 ga kungiyoyi na kasashen ketare da kuma maikata na iraqi don yin amfani dasu wajen sake gina kasar ta fannin tabbatuwar tsaro da dangogin su.

A can baya dai da yawa daga cikin masu sukar lamirin gwamnatin ta Bush sun soki lamirin gwamnatin nasa na cewa ta afkawa iraqi da yaki ba tare da kyakkyawan shiri ba,wanda a ganin su shine ummul aba,isin abin da yake faruwa a kasar a halin yanzu.

Bisa kuwa halin da ake ciki a kasar ta iraqi da Afghanistan ,Shugaba Bush ya kara da cewa a yanzu haka akwai sauye sauye da ake a rundunar sojin na Amurka ta yadda sojojin zasu tunkari kalubalen dake gaban su a wadan nan kasashe biyu bisa manufar cimma burin da aka sa a gaba.

Har ilya yau a lokacin jawabin nasa Shugaba Bush ya bukaci kasashen larabawa da kuma na sauran wasu nahiyoyi dasu rungumi mulkin dimokradiyya a tsayin turbar gudanar da al,amurran su na yau da kullum.

A waje daya kuma Bush ya bayyana cewa babban jibo da gwamnatin sa tasa a gaba a halin yanzu a wan nan karo na biyu shine fafutikar ganin kasashen duniya sun rungumi mulki irin na dimokradiyya.

Idan dai za a iya tunawa a makon daya gabata ne Shugaban na Amurka ya kai ziyara izuwa Nahiyar turai don gabatar da wan nan kudiri nasa.

A karshen jawabin nasa Bush ya yabi himma da kasashen Poland da Latvia da Lithunia ke nunawa wajen ganin mulkin dimokradiyya ya samu wanzuwa a kasar Belarus.