1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Georges Bush a game da ƙasar Irak

May 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buzv

A jawaban da ya saba yi, lokaci zuwa lokaci, shugaban ƙasar Amurika, Georges Bush, ya bayyana halin da ake ciki a Irak, a matsayin wani ci gaba mai tasiri, bayan da a ka zaɓi Nuri al- Maliki, a matsayin saban Praminista.

Bush yayi wannan jawabi, a yayin da ya gana da sakatariyar harakokin waje Condolesa Rice, da sakataran tasaro Donald Rumsfeld, wanda su ka dawo daga ziyara a ƙasar Irak.

A ɗaya hannun kuma, shugaba Bush, ya tuntuɓi takwaran sa, na Rasha, Vladmir Putin,ta wayar tarho, inda su ka tantana, a kan rikicin makaman nuklear ƙasar Iran.

Georges Bush, ya buƙaci goyan baya, daga Rasha, domin ɗaukar matakan hukunta Iran.

Gobe ne, idan Allah kai mu, a birnin Paris na ƙasar France, za a sake ganawa, tsakanin ƙasashe 5, masu kujerun dindindin, a komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, gami da Jamus, domin tsaida mattakan bai ɗaya a kan wannan rikici.