1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkozy Europa-Parlament

Hagendorn, Anke (DW Brüssel) NEUJuly 10, 2008

A matsayin sa na saban shugaban Ƙungiyar Tarayya Turai, Nikolas Sarkozy ya gabatar da jawabi a Majalisar Dokokin EU dake Strasbourg.

https://p.dw.com/p/Ea2F
Sarkozy na jawabi a Majalisar Dokokin EUHoto: picture-alliance/dpa


Shugaban Majalisar DokokinTurai kenan Hans-Gert Pöttering yayi lale marhabin da saban shugaban Ƙungiyar Tarayya Turai Nikolas Sarkozy a cikin taɓi da rahar´yan Majalisar EU.

Sarkozy ya taɓo batuwa da dama masu mahimmanci a cikin jawabin da yayi, hasali ma, haɗin kan turai da kuma  kundin tsarin mulkinta wanda a watan da ya gabata, al´ummar ƙasar Irland suka yi wasti da shi, matakin da ya hadasa saban ruɗami a tafiyar da harakokin mulkin EU.

Nikolas Sarkozy yayi bitar matakai dabam dabam da aka bi, kamin kaiwa ga yarjejeniyar Lisbonne da shugabanin EU suka amince da ita, a matsayin kundin tsarin mulki, ya kuma bayyana matsayinsa a game da makomar kundin , bayan watsin da Irland tayi da shi, tare da cewar:

babu wani saban taro da za mu shirya a dangane da kundin tsarin mulkin turai, kuma ba zamu ɓullo da saban kundi ba.

Ranar 21 ga watan da muke ciki, Sarkozy  ya alƙawarata kai ziyara a  Irland domin tattawa da magabatan ƙasar  a game da hanyoyin cimma yarjeniyar a game da kudin tsarin mulkin EU.

Zai gabatar masu da shawarwari wanda a cewar sa ke matsayin mafita daga wannan baddaƙƙala.

Batun ɗumamar yanayi na daga sahun gaba na jawabin Nikolas Sarkozy, inda ya bayyana aniyar Ƙungiyar EU na yin aiki wurjanjen tare da haɗin gwiwar sauran ƙasashen duniya, domin rage yawan iskan Gaz dake hadasa ɗumamar yanayi, yace a matsayinmu na al´ummomin dake raye a wannan zamani, zamu iya kauce duniya daga masifar ɗumamar yanayi.

Idan ba mu aiwatar da komai ba, to wanda za su biwo bayanmu ba za su iya hana abkuwar matsalolin ba.

Nikolas Sarkozy, yace ko shakka babu, a tsawan watanni shida zai riƙe ragamar Ƙungiyar Tarayya Turai, zai himmantuwa domin bada gundumuwa a game da batun  rage ɗumamar yanayi.

Wani daga baben da Nikolas Sarkozy ya ambata maida hankali akai, shine matsalar baƙin haure dake kwarara daga ƙasashen duniya zuwa Turai, ya bayyana ɗaukar mataki domin taƙaita al´amarin:

Turai ba za ta ƙin amincewa ba da karɓar baƙi daga ƙetare wanda ke bukatar aiki, to amma Turai ba zata iya karɓar duk masu buƙata ba shiga a cikin ta.

A tsakiyar shekara mai zuwa za a gudanar da zaɓɓuɓukan ´yan majalisar Tarayya Turai, da na hukumar zartaswa,  a game da haka Nikola Sarkozy ya bada goyan baya ƙarara, ga shugaban hukumar zartaswa na EU mai ci yanzu, Jose Manuel Barrosso domin yayi tazarce.

A ɗaya wajen Nikolasa Sarkozy ya bayyana aniyarsa ta halartar bikin buɗe gasar Olympic ta duniya, duk da adawar da ƙasar China da kuma kuma wani sashe na ´yan Majalisar Dokokin EU suka nuna.