1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

JAWABIN SHUGABA ARAFAT WA MAJALISAR DOKOKIN PALASDINU.

August 18, 2004

Shugaban Palasdinawa ya lashi takobin yaki da rashawa da inganta tsaro a gwamnatinsa.

https://p.dw.com/p/BvhE
Shugaban Palasdinwa Mallam Yasser Arafat.
Shugaban Palasdinwa Mallam Yasser Arafat.Hoto: AP

Shugaban Palasdinawa Yasser Arafat dake cigaba fuskantar matsin lamba na raba madafan iko da prime ministansa da kawo sauyi cikin gwamnatinsa dake shan zargi,akaro na farko ya amince da kura kuren da yayi abaya,sai dai yaki ambaton wadannan kura kurai balle hanyoyi dazai bi na gyaransu.

Shugaban na Palasdinawa nacigaba da fuskantar adawa da suka dangane da yadda yake tafi da gwamnatinsa da aka danganta da Rashawa,wanda kuma ake ganin cewa ko kadan basu sha mai kai ba.A matsayinshi na shugaban Palasdinawa na tsawon shekaru 10,ana zargin Arafat da gazawa wajen yakan miyagun ayyuka,gyaran matakan tsaron yankin,tara da bawa wasu madafan iko,amaimakon yadda ya kasance wuka da nama kann kowane lamari daya shafi yankin.

Ayayinda Mallam Arafat yake wannan jawabi wa majalisar yankin,a zirin Gaza kuwa Dakarun Izraela sun tayar da wasu boma bomai a kusa da gidan wani dan kungiyar Hamas ,inda yayi sanadiyar mutuwan palasdinawa 5,tare da raunana wasu 7,ayayinda wanda aka kaiwa harin Ahmed Jabari,ya tsira da yan raunuka kalilan.

Wannan jawabin na Arafat ayau dai yazo ne adai dai lokacin da ake cigaba da korafe korafe a gabon yamma da kogin Jordan da zirin gaza,a dangane da yadda yake tafi da mulkinsa.A watan daya gabata nedai aka gudanar da zanga zanga kann titunan yankin domin nuna adawa da wasu mukamai daya bayar,wanda ya jawo barazanar yin murabus daga prime ministansa.

To sai dai a hannu guda wasu har yanzu na masa kallon gwarzon namiji,wanda shine kadai zai iya tabbatar da hadin kann yankin na Palasdinu,duk da korafi da ake cigaba dayi.

A martaninsa wa yan majalisar,Mallam Arafat yayi alkawarin yiwa gwamnatinsa gyaran fuska,wadanda suka bukaceshi daya basu tabbaci a rubuce.Ya dai amince cewa akwai rashawa tsakanin jamian gwamnati ,tare da alkawrin gurfanar da wanda aka kama da laifi gaban hukuma,kazalika zaa dauki tsauraran matakai na gyaran sashin tsaro na wannan yanki.

Daya daga cikin masu kalubalantarsa kuma tsohon minister Abdel Jawad Saleh,yace shi kanshi Arafat yana kare jamiai da ake zargi da rashawa a gwamnatinsa.Bayan shugaban ya kammala jawabinsa,Saleh yace ,jawabansa ba komai bane face buhun alkawura da bazai cika koda guda ba,inda yayi gargadin cewa nan bada jimawa ba zaa fuskaci tashe tashen hankula na adawa da gwamnatinsa .

Prime minista Ahmed Qurei,wanda a watan daya gabata yayi murabus na gajeren lokaci,saboda rashin bashi madafan iko,ya zauna shiru kusa da shugaban Palasdinawan,ayayin jawabin nasa.

Sai dai a harin Izraelan nayau yan kungiyar Hamas 3 suka rasa rayukansu,ciki kuwa harda da babban Dan Jabari,wanda aka kai harin dominsa,da kuma wani dan jihadil Islami.

Shi kuwa Minister Saeb Erekat ,zargin izraela yayi da ruruta rikicin yankin ta kai hare hare da fadada matsugunnen yahudawa yan kama wuri zauna.

Zainab Mohammed.