1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Singh aMajalisar Nigeria

October 15, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8O

Gyare gyaren da akeyi a komitin sulhun mdd bazai taba kammaluwa ba,idan baa bawa Afrika wakilci ba,inji Premiern India Manmohan Singh a birnin Abujan tarayyar Nigeria.Singh yayi wannan furuci ne a lokacin dayake jawabi wa hadin gwiwar majalisar tarayar Nigeria,a bangaren rangadin aiki dakeyi a wannan kasa dake mafi yawan alumma a nahiyar Afrika.Yace India na mika godiyar ta sakamakon irin goyon bayan da Nigeria ta bada,adangane da samun wakilci a komtin sunhun da aka fadada.Shugaban majalisar dottijan Nigeria David Mark ya lura dacewar India dake zama mai mafi girman Democradiyya a duniya da Nigeria dake da mafi yawan alumma a nahiyar Afrika,bayaga yawan alumma da yawan addinai,suna da makoma guda.Akan hakane yace,akwai abubuwa da dama da Nigeria zatayi koyi dashi ta fannin Democradiyya daga India.Ayayinda ita kuwa kakakin majlisar wakilai Patricia Etteh,tace dukkan yarjeniyoyin hadin gwiwa da kasashen biyu zasu shiga,zasu samu cikakken goyon bayan majalisar.