1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jean-Pierre Bemba ya amince da sakamakon zaben shugaban kasar Kongo

November 29, 2006
https://p.dw.com/p/BuZq

Tsohon madugun ´yan tawayen kasar JDK Jean-Pierre Bemba ya amince da kayin da ya sha a zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin watan jiya. Bemba ya ce yanzu zai koma matsayin dan adawa. Hakan dai ya zo ne bayan da kotun kolin kasar ta Kongo ta yi watsi da karar da ya shigar inda yake kalubalantar sakamakon zaben wanda shugaba Josef Kabila ya lashe. A cikin wata sanarwa Bemba ya ce zai ci-gaba da gwagwarmaya a matsayin dan adawa na siyasa don samar da zaman lafiya da hade kan kasar. Masu sa ido a zabe na kasa da kasa sun ce an kamanta gaskiya da adalci a zaben wanda shi ne irinsa na farko da aka gudanar a Kongo tun bayan shekarar 1955.