1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya aika sunayen 'yan majalisar ministoci Majalisa

Ubale Musa/MNASeptember 30, 2015

Kasa da 'yan sa'o'i da cikar wa'adin 30 ga watan Satumba Shugaba Buhari ya mika sunayen jerin ministocin da yake fatan za su taimaka masa mulki ga majalisar kasar.

https://p.dw.com/p/1GgEC
Paris Medef Zentrale Buhari Gattaz
Hoto: Getty Images/AFP/E. Piermont

Duk da cewar dai babu dalla dallar ko su wane ne, wata tawagar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, karkashin jagorancin babban Hafsan mulkin fadar Shugaban kasar Alhaji Abba Kyari ta kai sakon ga shugaban majalisar Abubakar Bukola Saraki da yammacin ranar Laraba.

Shi ma dai shugaban majalisar ya tabbatar da karbar sunayen a shafinsa na Twitter da kuma nuna hoton takardar da ke dauke da sunaye na ministocin. Abin kuma da ya kawo karshen zaman jiran wattani hudu da ma zaman dardar din da ya mamaye daukacin kasar ta Najeriya.

To sai dai kuma sai kila zuwa cikin dare ne ake saran sanin daukacin sunayen da ma kila rawar da kowane zai taka a kokarin ginin kasar.

Sako a cikin jawabin bikin zagayowar ranar 'yancin kai

To sai dai abu guda da ya fito fili na sunayen na zaman wani bangare na ministocin a yayin kuma da shugaban zai aike da wani bangaren kamar yadda wani jawabin da yake shirin karanta wa 'yan kasar a ranar Alhamis don 'yancin kai ya ambato.

Nigeria Bukola Saraki
Bukola Saraki Shugaban majalisar dattawan NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Senator Bala Na'Allah da ke zaman mataimakin shugaban masu rinjayen majalisar kuma a fadarsa za su tabbatar da kallon tsaf ga sunayen kafun kaiwa ga amince wa da su a nan gaba.

Ana dai ta'allaka rashin tafiyar harkoki cikin kasar da ma kila rashin kudi a hannun jama'a da gazawar shugaba Buhari na kafa majalisar mai tasiri a tsakanin al'umma.

To sai dai a tunanin Dr Nazifi Abdullahi Darma da ke zaman masanin tattalin arzikin kasar "ba wani banbanci ga kasar a tsakanin nadin ministocin da kuma tafi da harkokin mulki da ma'aikatan da gwamnatin ta share watanni hudu kansa zuwa yanzu"

To sai dai kuma karkashin sabon tsarin da gwamnatin ke shirin fitarwa kowane lokaci ya zuwa yanzu. Shugaba Buharin ne kuma zai zamo ministan man fetur na kasar a wani abinda 'yan sharhi ke kallon kokari na kai karshen cin hancin da yai aure ya kai ga tarewa cikin masana'antar.