1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jigogin taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar NATO

Mohammad Nasiru AwalDecember 9, 2004

Taron ministocin harkokin ketare na kasashen kungiyar tsaro ta NATO a birnin Brussels zai fi mayar da hankali kan Iraqi da Afghanistan.

https://p.dw.com/p/BveG
Hedkwatar kungiyar NATO a birnin Brussels
Hedkwatar kungiyar NATO a birnin BrusselsHoto: NATO

Tun wasu watanni da suka wuce ake yi ta jin cewar kungiyar tsaro ta NATO.ta kawo karshen bambamce-bambamcen ra´ayi da kuma rashin jituwa da aka fuskanta tsakanin membobinta dangane da yakin kasar Iraqi. Domin a wancan lokaci kasashe kamar Jamus da Faransa da Spain sun ce ba zasu shiga cikin duk wani aikin horaswa da ake shirin yi a cikin kasar Iraqi ba. Hakazalika kasashe sun ce ba zasu ba da gudummawar sojojinsu ga wata rundunar da NATO zata tura Iraqi ba. Ko kadan Amirka ba ta ji dadin haka ba. A dangane da haka sakatare janar na NATO Jaap de Hoop ya nunar da cewa babbar manufar kafa wannan kawance na fuskantar barazana ta rugujewa.

Bugu da kari an fuskanci wata sabuwar takaddama dangane da kasar Afghanistan, bayan zargin da Amirka ta yi cewar ana samun tafiyar hawainiya wajen tabbatar da zaman lafiya a wajen birnin Kabul, musamman a aikin sake gina wannan kasa inda ake hadin gwiwa tsakanin sojoji da kuma kungiyoyin fararen hula. Ko da yake Amirka ta yi tayin ba da karin wakilai, amma a lokaci daya ta yi kira ga kawenta na Turai da su ma su bi sahunta.

A batutuwan da suka shafi kasashen biyu wato Iraqi da Afghanistan, Amirka na neman a hanzarta tare da fadada aikin sake gina kasashe. To amma burinta shine ta kara dorawa kungiyar NATO wannan nauyi. Sai dai har yanzu ba ta samu nasara bisa wannan manufa ba, domin daukacin kasashen nahiyar Turai ba su yi amanna da manufofin ketare na shugaba George W Bush ba. Akan wadannan batutuwan ne za´a shawarta tsakanin ministocin harkokin ketare na NATO da takwaransu na Amirka Colin Powell mai sassaucin ra´ayi. Wannan taron na birnin Brussels zai kasance na karshe ga mista Powell a matsayinsa na sakataren harkokin wajen Amirka. Masharhanta sun nunar da cewa sabuwar sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleeza Rice ba kamar mista Powell ba, ita kam ba zata nuna sassauci ga takwarorinta na Turai ba.

Wani batun da ra´ayi ya zo daya a cikin kungiyar ta NATO shine game da kasar Ukraine bayan zaben shugaban wannan kasa da aka yi ta kai ruwa rana kai. Ministocin harkokin wajen na NATO sun soke wani taro da aka shirya yi da takwaransu na na Ukraine, don nuna rashin amincewarsu ga sahihancin gwamnatin kasar. To sai dai hakan ya batawa Rasha rai, kasar da ta kulla wata yarjejenya ta musamman ga kungiyar ta NATO. A dangane da haka za´a sake fuskantar juna tsakanin ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov da mista Powell, wadanda a kwanakin baya suka zargi juna da tsoma baki a harkokin cikin gidan Ukraine.

Duk da haka dai wannan taron zai kasance mai muhimmanci ga kungiyar ta NATO wadda ke kokarin daga martabarta a kasashen Larabawa, musamman a yakin da ake yi da ta´addanci da kuma kokarin yin sulhu tsakanin Isra´ila da Falasdinawa.