1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Mujaddadi Shehu Usman Dan fodiyo.

Kamaluddeen SaniOctober 7, 2015

An haifi Shehu Usman Dan Fodiyo da ake cewa Shehu Usman Ibn Fodiyo Mujaddadi a shekara ta 1754 a wani Gari mai Suna Gobir a Sokoto.

https://p.dw.com/p/1Gk8H
Nigeria Ramadan
Hoto: picture-alliance/AP Photo/G. Osodi

wanda ya jaddada addinin musulunci a kasashen Hausa da makawaftan su da kewaye.Shehu wanda ke zama dan kalibar Fulani shine kuma ya samar da daular musulunci ta dake Jihar Sokoto da aka fi sani da Sokoto Caliphate,Dan fodiyo ya kasance jagora wanda ke bin mazahabar Sunni.

To yaya batun Iyalan sa fa:

Baya ga Abdullahi dake zama dan uwan sa na jini sai futattun 'yayan sa watou Muhammad Bello da Nana As'mau.

Ita kanta As'mau marubuciya ce kamar ragowar yan uwanta. Asmau tayi tafiye- tafiye masu dumbum yawa domin koyar da mata ilimi,mafi yawancin littatafan ta sun kunshi ilimin addinin Islama kuma tana jin yarukan Fulfulde da Hausa da Arabiyya da yaren Tamachek kamar dai yadda David Westerlund fitattecen marubuci ya nunar da cewar As'mau na cigaba da kasancewa wata tauraruwa a tsakanin mata har yanzu a kasashen Hausa.

To ko shin Menene ya sanya Shehu gudun hijira dashi da tawagar sa:

A sakamakon irin gallazawar da jagororin wancen lokacin suke yiwa jama’ah tare da rungumar akidun maguzanci na wanna lokacin.wannan ne ma babban dalilin gudun hijirar su.

Kazalika hijirar nada alaka da jaddada addinin musulunci da kuma kawo sauyi ta fuskar siyasa da zamantakewa a tsakanin al'umma kuma sauyin ya fara ne ta fara ne daga Gobir zuwa a kasashen da a yau ake kira Nijeriya,Niger da Kameru.

To yaya batun irin littattafan daya rubuta a lokacin da yake raye:

Dan fodiyo ya rubuta daruruwan littattafai da suka hada da na addini,harkokin gwamnati da mulki,al'adu da kuma al'amuran da suka shafi yanayin kasa,ya kuma soki lamirin wasu daga cikin shugabanin addini a wancen lokacin ganin yadda suka yi watsi da koyarawar addinin musulunci tare da rungumar bokanci da tsibbu wanda hakan yayi karen tsaye ga dokokin addinin Islama.

yayi tir da irin yadda jagororin wancen lokacin suka dunga tsanantawa mutane ta wajen sanya musu haraji mai tsanani.

To ko yaya fafutukar sa a bangaren Jihadi:

A karni na 17 da 18 da 19 Dan fodiyo ya taka muhimiyar rawa wajen bunkasa addinin musulunci tare da samun nasarar jihadi a Futa Buntu da Futa Toro da Fouta Djallon a tsakanin shekarun 1650 zuwa 1750 wanda ya haifar da jihohi uku na musulunci. Shehu ya zama abin kwaikawayo ga sauran musu jaddada jihadi a Afrika irin su Seku Amudu wanda ya samar da daular Masina da El-Hadj Umar Tall daya samar da daular Toucouler wanda kuma daga bisani ya auri daya daga cikin jikokin Shehu da kuma Modibo Adama daya samar da daular Adamawa ta Najeriya .

Wadanne garuruwa ne Shehu ya jaddada musuluncin:

A kwai Kano,da Kastina da Zariya da Borno da Gombe da Adamawa da yankunan Nupawa da Ilorin Kwara sai wasu yankuna a Jamhuriyar Niger da Kameru. Muhammad Bello da dan uwansa Abdullahi sun taimaka masa sosai wajen jaddada jihadi tare da tafiyar da sha’anin mulki bayan shekara ta 1811 Shehu yayi ritaya da harkokin mulki tare da cigaba da rubuta littatafai.

Shehu Mudaddadi ya koma ga Allah a shekara ta 1817.