1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jimmy Karter ya soki Bush da zubda mutunci Amurika

November 2, 2005
https://p.dw.com/p/BvMn

Tsofan shugaban kasar Amurika Jimmy Karter ya soki gwamnatin Shugaba Bush, mai ci yanzu da bata sunan Amurika da Amurikawa, da kuma wargaza tushen mutunci da karamci da dunia ta san Amurika da su a shekarun baya.

Jimmy Karter da ya jagoranci Amurika daga 1977 zuwa 1981 ya nuna matukar takaici, a game da zubda mutuncin Amurika da Bush ke yi a idon dunia, da sunan yaki ta ta´adanci, da abubuwa makamantan haka.

Ya ce a game da hujjojin da Amurika,ta bada na kai hari ga kasar Iraki hujjoji ne marasa tushe da a ka kirkiro don yaudara Amurikawa.

Masharahanta na bayyana cewa,Kalamomin tsofan shugaban kasar ta Amurika, za su kara nutsa Georges Bush cikin ruwan da ke shirin cimmasa a yan kwanakin nan.