Jiragen Rasha sun yi shawagi a kan wani jirgin ruwan Amirka
April 13, 2016Talla
Wani babban hafsan sojin ruwa na Amirka wanda bai so a bayyana sunana ba wanda ya ce hakan bai dace ba kana kuma ya ce abu ne da ke cike da hadari.Ya ce tun daga ranar Litinin har zuwa Talata jiragen na sama na Rasha samfarin SU-24,ke yin shawagi a kan jirgin yaƙin na Amirka USS Donald COOK wanda daga sama tazarar da ke tsakaninsu ba ta wuce mita 30 ba.Ya kuma ƙara da cewar jiragen guda biyu na Rasha sun yi ta kai da kawo a kan jirgin ruwan har kusan so 20 kusa kwarai daga ƙasa-ƙasa:
A kwanakin baya-baya nan dai dangantaka tsakanin Amirkan da Rasha ta yi tsauri saboda rikicin Siriya da kuma Ukraine.