1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiragen sama sun soma jigilar fasinjoji a Nahiyar turai

April 20, 2010

Kamfanonin jiragen sama na turai sun fara jigilar fasinjojin daga nahiyar Turai

https://p.dw.com/p/N1Uy
Wani jirgin saman a ƙasar Indiya da ke shirin tashiHoto: AP

Duban fasinjojin cikin miliyoyin da suka maƙalle a filayen saukar jiragen sama na Turai sun samu tashi cikin jirage a yau ko´ina daga ƙasashen Turai, bayan da suka shafe ƙwanaki shidda cikin tsaiko a sakamakon gajumarai na toka da ya mamaye sararin samaniyar Turai akan aman wuta da wani tsaunin ke yi a ƙasar Ayisla.A Faransa an bada rahoton cewa wasu fasinjojin daga birnin New York sun samu isowa a filin saukar jiragen Roissy, yayin da yanzu haka wasu 200 ke can suna jira sannan a ƙasashen Beljiam ,da Nowe,da Spain, da Italiya  duk sun soma zirga zirga ƙaɗan ƙaɗan . Kamfanin sufurin jiragen sama na Delta Arilines na Amurka ya ce ya tabka asara da ta kai ta dala Amurka milliyan 20 yayin da kamfanin Eimirat na Dubai ya ɓatar da dala milliyon 65 na Amurka.

Mawallafi:  Abdourahamane Hassane

Edita       :  Yahouza Sadissou Madobi