1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiragen saman yaƙin Isra’ila sun sake keta dokar ƙasa da ƙasa da kutsawa cikin sararin samaniyar ƙasar Lebanon.

November 17, 2006
https://p.dw.com/p/BubV

A wata sabuwa kuma, mun sami rahotannin cewa, jiragen saman yaƙin Isra’ila sun sake kutsawa cikin sararin samaniyar ƙasar Lebanon, duk da sukar da gamayyar ƙasa da ƙasa suka yi ga irin wannan kutsawar a kwanakin bayan nan. Rahotannin sun ce jiragen saman Isra’ilan guda uku ne suka yi shawagi a sararin samaniyar biranen Tyre da Bint Jbeil, da sanyi safiyar yau, kuma a yankunan da dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya ke girke.

Ƙasar Bani Yahudun dai ta sha kutsawa cikin Lebanon ɗin, duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cim ma a ran 14 ga watan Agusta, don kawo ƙarshen fafatawar da aka shafe wata ɗaya ana yi tsakaninta da ƙungiyar Hizbullahi ta ƙasar Lebanon.

Da aka yi wa wani kakakin rundunar sojin Isra’ilan tambaya game da kutsawar ta yau, cewa ya yi, ba sa ba da bayanai kan harkokin mayaƙan samansu.

A watan jiya ne dai ministan tsaron Isra’ilan Amir Peretz ya nanata cewa, kutsawar da jiragen saman ke yi a Lebanon na da muhimmanci ƙwarai, saboda tana ba su damar bin diddigin sumogan makaman da ƙungiyar Hizbullahin ke yi.